An shiga fargabar sace fitattun jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kudancin Nijeriya wato ‘Nollywood’ Cynthia Okereke da Clemson Cornell, bayan sun kammala daukar wani shirin fim a jihar Enugu a ranar Juma’a yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida amma an nemesu sama da kasa an rasa.
Mai magana da yawun kungiyar jarumai a masana’antar, Monalisa Chinda, ce ta tabbatar da hakan a shafinta na Instagram.
- Kwakwanso Ya Gargadi Sanatoci Kan Barazanar Tsige Buhari
- ‘Yansanda Sun Ceto Mutum 42 Daga Masu Garkuwa A Kano
Chinda ta bayyana cewar manyan abokan kasuwancinta na harkar fina-finai din an shiga fargabar yin garkuwa da su ne bayan da iyalansu suka tabbatar da cewar ba su dawo gidajensu ba tun bayan barin wajen daukan wani fim a yankin Ozalla da ke jihar Enugu.
“Ana zargin an yi garkuwa da fitattun jarumai biyu don dole masu shirya fina-finai su kara kula da harkokin tsaronsu a fadin kasar nan.
“Kan wannan matakin, shugaban kungiyar, Ejezie Emeka Rollas, ya umarci dukkanin jarumai da su daina zuwa daukan fim a wuraren da babu cikakken tsaro.
“Shugaban ya nuna kaduwarsa bisa wannan lamarin tare da jawo hankalin hukumomin tsaro da su yi kokarin gudanar da bincike tare da tabbatar da lafiyar jaruman tare da kubutar da su cikin koshin lafiya.
“Sannan ya kuma roki jama’a da su yi addu’ar Ubangiji ya kubutar da jaruman,” a cewar sanarwar.