Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gargadi ‘yan majalisar dokokin kasar da su bi a hankali kan matakin da wasu daga cikinsu ke yunkurin dauka na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Kwakwanso ya yi wannan gargadin ne jim kadan bayan ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq a fadar gwamnati da ke Ilorin babban birnin jihar.
- Amurka Ta Kau Da Kai Daga Aikin Tilas Da Fataucin Mutane Cikin Daruruwan Shekaru!
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutun 6, Sun Bukaci Miliyan 50 Matsayin Kudin Fansa A Katsina
Kwankwaso, ya ce bai kamata Sanatocin su yi gaggawar girgiza shugaban ba, ko da yake ya ce “suna da dalilan da za su damu tun da batu ne na matsalar tsaro a kasar.”
Kwakwanso, ya bukaci gwamnati da ta jajirce wajen tunkarar kalubalen rashin tsaro a fadin kasar nan.
Ya jaddada bukatar gwamnati ta tuntubi mutanen da ke da matukar damuwa kan matsalolin da ke addabar al’umma da nufin lalubo hanyoyin magance kalubalen.
Shi ma da yake jawabi gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi kira ga ‘yan siyasa da su rika yin siyasa kamar yadda doka ta tanada.
Ya kuma bukace su da guci tashin hankali wajen yakin neman zabe gabanin babban zaben 2023.