Tun daga yau Talata, an fara haramar tafiye-tafiye, kwanaki 15 gabanin zuwan ranar farko ta Bikin Bazara na al’ummar Sinawa na bana.
Ranar ta zamo ta farko cikin ranakun da ake yiwa lakabi da “Chunyun,” wato lokacin rububin tafiye-tafiye masu nasaba da Bikin Bazara na sabuwar shekarar kasar Sin bisa kalandar gargajiyar kasar, tun bayan da hukumar UNESCO ta ayyana Bikin Bazara, a matsayin daya daga cikin al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba, wadanda aka gada daga kaka da kakanni, a watan Disamban shekarar bara.
- Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Ɓangaren Bafarawa Kan Rikicin Shugabannin PDP A Sakkwato
- Huldar Sin Da Afirka Za Ta Zama Abin Koyi Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Daukacin Bil’adama
Ana hasashen cewa a bana, yawan tafiye-tafiye masu nasaba da bikin za su iya kaiwa biliyan 9, tun daga yanzu har zuwa ranar 22 ga watan Fabarairu dake tafe, inda ake sa ran ganin tafiye-tafiye ta jiragen kasa, da na sama za su kai wani sabon matsayi a tarihi.
A kasar Sin, ana samun karuwar zirga-zirgar fasinjoji cikin kwanaki 40, wadanda ke da nasaba da shagulgulan bikin sabuwar shekarar kasar, inda daruruwan miliyoyin mutane ke komawa zuwa garuruwansu na asali, domin saduwa da iyalai. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)