Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da ware kwanaki uku da zai fara aiki daga ranar Talata domin juyayi bisa kisan fararen hula 50 a karshen mako a arewacin kasar.
Jagoran sojin kasar, Lieutenant Colonel Paul-Henri Damiba shi ne ya sanar da hakan, ya ce kasar za ta nuna alhini da juyayi na wannan mummunar lamarin.
- Kotu Ta Saka Ranar Yanke Hukunci Akan Wanda Ake Zargi Da Kashe Hanifa
- Kotu Ta Yanke Wa DCP Abba Kyari Da Wasu Mutum 2 Hukuncin Daurin Shekaru 2 A Gidan Yari
A ranar Litinin gwamnati ta ce fararen hula 50 ne aka kashe a harin da wasu ‘yan bindiga dadi da ba a tantance ko suwaye ba su kai a yankin Seytenga. Kodayake wasu rahotonni sun ce adadin mutuwar ma ya zarce mutum 100.
A tsawon kwanakin juyayin za a sauke tutucin kasar a dukkanin muhallan gwamnati domin nuna juyayi.