Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa a tarihinsa bai taba shan kaye a zabe ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin gangamin jam’iyyar APC wanda ya gudana a Jihar Ekiti kafin zaben gwamna a jihar, domin jawo hankalin magoya bayan jam’iyyar su zabi dan takarar gwamna, Biodun Oyebanji.
Tinubu ya ce, “Ban taba faduwa zabe ba tun da nake a siyasata.” Cewarsa.
Ya dai bayyana hakan ne a cikin harshen Yarbanci tare da cewa idan mutum bai yi zabe ba, to ba zai taba samun kudade masu yawa ba.
Haka kuma ya siffanta PDP a matsayin jam’iyya mai bunkasa talauci, inda ya bukaci daukacin mutanen jihar su zabi APC a zaben gwamna da kuma na shugaban kasa a 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp