Duk da rashin samun cikakken rahoto a kan sanin sabuwar cutar da ta barke makwanni biyu da suka wuce a Jihar Zamfara, wadda ta yi sanadiyyar asarar rayuka; yanzu haka, ana ci gaba da samun saukin yaduwarta, wadanda kuma suka kamu da ita, na ci gaba da karbar magani a wurin da aka kebe su.
Har bayan kammala hada wannan rahoto, ana ci gaba da dakon Hukumar Kula da Yaki da Cututtuka da ke Jihar Legas da Abuja, don sanin asalin wannan cuta da ta kunno kai wannan jiha.
- Gwamnan Zamfara Ya Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi Daga N7,000 Zuwa N30,000, Za A Fara Biya Daga Yuni
- Tinubu Zai Halarci Bikin Rantsar Da Mahamat Deby A Chadi
Idan za a iya tunawa dai, wannan sabuwar cuta da aka kasa sanin gabanta da bayanta, ta yi sanadiyar mutuwar mutum 13, yayin da kuma sama da mutum 500 suka kamu da ita, inda kuma rahoton bullar cutar ya tabbatar da cewa; cutar ta fi shafar yara kanana da mata a garuruwa da dama na fadin jihar ta Zamfara.
Wata majiya daga ma’aikatan lafiya ta tabbatar da cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ne, a Kauyen Tsibiri da ke Karamar Hukumar Maradun, aka fara samun bullar wannan cuta a cikin watan Fabrairun wannan shekara da muke ciki, sannan kimanin mutum hudu sun rasa rayukansu; sakamakon kamuwa da wannan cuta, yayin da kuma mutum 228 suka kamu da cutar.
Kazalika, daga cikin wadannan mutane da suka kamu da cutar, mutum 10 sun yi matukar fuskantar matsananciyar wahala, inda aka tura su zuwa Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Shehu Shagari da ke Gusau; babban birnin jihar, a cewar ma’aikatan lafiyar.
Majiyar ta kara da cewa, cutar ba wai kawai ta ci gaba da wanzuwa a tsibiri ba ne kadai, ta yadu har zuwa wasu yankunan da suka hada da Kananan Hukumomin Shinkafi, Gusau, Zurmi da kuma Karmar Hukumar Isah da ke Jihar Sokoto, wadda ta yi iyaka da Zurmi.
A Kauyen Galadi na Karamar Hukumar Shinkafi, wadanda suka kamu da cutar sun fara ne da zazzabi mai tsanani da ciwon ciki, kamar yadda wani Ma’aikacin Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHC) ya bayyana.
“Mun samu rahoton fiye da mutum 100, wadanda suka kamu da cutar tare da mutuwar mutum shida, ban da kuma sauran marasa lafiya fiye da mutum 60 da aka garzaya da su zuwa manyan wuraren da aka kebe; don kula da tasu lafiyar, a cewar rahoton.
“Ko shakka babu, yaduwar wannan cuta; ta yi matukar haifar da kiraye-kiraye ga Gwamnatin Jihar Zamfara cikin gaggawa, kan bukatar karin kwararrun likitoci a wannan fage, domin shawo kan wannan sabuwar cuta da aka kasa sanin kanta kafin ta kai ga hallaka al’umma baki-daya,” in ji wani jami’in kiwon lafiya.
Musa Salisu, wani mazaunin Maradun wanda ya yi matukar kaduwa bisa barkewar wannan cuta tare kuma da jin tsoron yiwuwar fantsamar cutar zuwa wasu yankunan da ‘yan bindiga ke iko, wanda hakan zai iya haifar da tarnaki wajen kai musu agajin gaggawa.
Kwamishiniyar lafiya ta Jihar Zamfara, Dakta A’isha Anka, ta yi karin bayani a kan alamomin wannan cuta mai ban mamaki, inda ta ce; “marasa lafiya na fama da matsalar kumburin ciki, tarin, zazzabi da kuma kasala, mai yiwuwa saboda gurbataccen ruwa.
Yanzu haka dai, tuni jihar ta kai rahoton bullar cutar ga Hukumar Yaki da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC), tare da bayar da hadin kai kan matakan da suka kamata a dauka na gaggawa.
“Mun aika da samfura zuwa dakunan gwaje-gwaje a Legas da Abuja, domin tantancewa da kuma tsara shirin shawo kan barkewar wannan cuta.
Ta kara da cewa, “mutane hudu sun rasa rayukansu, 177 kuma sun kamu da wannan sabuwar cuta da bulla a wannan jiha tamu ta Zamfara”, in ji Anka.
LEADERSHIP Hausa, ta yi kokarin jin ta bakin Jami’an Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Bello Boko, amma abin ya ci tura; inda ya bayyana cewa, sai dai a nemi, Daraktan Lafiya na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Zamfara, Dakta Yusif Abubakar.