Wani mummunan al’amari ya faru da wani sabon ango mai suna Dan Gaske Mai Masara, bayan da amaryarsa ta soke shi da wuƙa a wuya, wanda ya yi sanadin mtutrwasa a kauyen Tashar Aibo, Ƙaramar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.
An daura aurensu ne a Alhamis, 18 ga watan Nuwamba, 2025, amma wannan aure ya ƙare da takaici a ranar Lahadi, bayan amaryar ta hallaka mijin nata har lahira.
- Rashin Tsaro Zai Haifar Da Mummunar Yunwa A Arewacin Nijeriya – Majalisar Ɗinkin Duniya
- ’Yan Majalisar Kudu Maso Gabas Sun Roƙi Tinubu Ya Yi Wa Nnamdi Kanu Afuwa
A cewar mazauna unguwar, matar ta kai wa mijinta hari da wuƙa yayin da yake barci, ta soke shi a wuya, wanda hakan ya yi sanadin ajalinsa.
ADVERTISEMENT
Har yanzu ba a san dalilin da ya sa ta aikata hakan ba, kuma hukumomi ba su fitar da sanarwa kan game da lamarin ba.














