La Liga ta kira kwararren da zai fassara mata kalaman da dan wasa Jude Bellingham ya yi ta hanyar motsa lebe da ake zargin ya ci zarafin dan wasan Getafe, Mason Greenwood.
Hukumar dake kula da gasar La Liga ta sanar cewar Getafe ce ta shigar da korafi, saboda haka za ta yanke hukunci ta sauraren shaidun da suka ji abin da dan kwallon Real Madrid din ya fada da kuma abin da kwararru suka bankado.
- Abuja Na Fuskantar Baranazar Tsaro -Majalisar Dattawa
- Yadda Nijeriya Ta Taka Rawar Gani Har Zuwa Zagayen Karshe Na Gasar AFCON
Lamarin ya faru ne, bayan dan wasan tawagar Ingila, Bellingham ya yi wa Greenwood keta a gasar La Liga da Real Madrid ta yi nasara 2-0, sai dai har yanzu kungiyar ta Real Madrid ba ta ce komai ba a kan zargin da ake yi wa babban dan wasan nata.
Greenwood, mai shekara 22, ya koma Getafe kan yarjejeniyar buga wasannin aro zuwa karshen kakar wasa ta bana daga kungiyar Manchester United daga 1 ga watan Satumban shekarar da ta gabata.
Cikin watan Agusta, Manchester United ta sanar cewar dan kwallon zai motsa, sakamakon da suka cimma matsaya, bayan da aka kammala bincikensa wata shida kan laifin cin zarafin wata mata.
Daga baya ne aka soke dukkan tuhume-tuhumen da aka yi wa Greenwood a cikin Fabrairu, da ya shafi fyade da cin zarafi kuma Greenwood, wanda yake da kunshin yarjejeniya a Manchester da za ta kare a 2025, ya ci kwallo shida a wasa 21 a kakar nan.
Dan wasa Bellingham, mai shekara 20, ya koma Real Madrid kan fara kakar bana kan kudi fam miliyan 88.5, wanda ya ci kwallo 18 a wasanni 27 a kungiyar Santiago Bernabeu.