Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray ta ce za ta fara gudanar da bincike kan kocin Fenerbahce Jose Mourinho bayan da ta zarge shi da furta kalaman wariyar launin fata bayan da ƙungiyoyin suka tashi 0-0 ranar Litinin.
Zuwa yanzu dai ba a bayyana irin kalaman da Galatasaray ke nufin Mourinho da furtawa ba, da yake magana a taron manema labarai bayan kammala wasan derby na Istanbul, Mourinho ya ce kujerar da ya zauna a filin wasan Galatasaray ba ta zama kurum, ta na tsalle kamar biri idan aka zauna kanta, ya kuma sake nanata sukarsa ga alƙalan wasan Turkiyya, yana mai cewa da an tafka babban kuskure idan akayi amfani da wani alkalin wasan ƙasar a wasan.
- An Dakatar Da Mourinho Wasanni 4 Kan Fada Da Alkalin Wasa
- Roma Ta Sallami Mourinho A Matsayin Kocinta
Ɗan ƙasar Slovenia Slavko Vincic ne ya jagoranci wasan na ranar Litinin bayan ƙungiyoyin biyu sun buƙaci wani jami’in ƙasar waje ya jagoranci wasan, kazalika barazanar ɗaukar matakin shari’a, Galatasaray ta ce za ta gabatar da “ƙorafe-ƙorafe a hukumance” ga hukumomin ƙwallon ƙafan ƙasar Turkiyya.
A cikin wata sanarwa da Galatasaray ta fitar ta ce tun daga lokacin da ya fara gudanar da aikinsa a ƙasar Turkiyya, kocin Fenerbahce Jose Mourinho na ci gaba da furta kalaman batanci ga al’ummar Turkiyya, an nada Mourinho mai shekaru 62 wanda ya lashe gasar zakarun Turai sau biyu a matsayin kocin Fenerbahce a bazarar da ta wuce kuma an dakatar da shi da kuma cin tarar shi a farkon wannan kakar saboda yin Allah wadai da ƙa’idojin alƙalan wasa a Turkiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp