Andrei Okounkov, wanda ya lashe lambar yabo ta Fields Medal, da ake bayarwa a fagen lissafi, ya bayyana Sinawa a matsayin masu bayar da muhimmanci ga koyon abubuwa, yana mai cewa wannan shi ne muhimmin dalilin da ya sa kasar ke ci gaba da samun nasarori a bangaren kimiyya da fasaha.
Andrei Okounkov ya bayyana haka ne yayin zantawarsa da kafar CMG, lokacin da yake halartar taron kasa da kasa karo na 3 kan tubalin kimiyya a kasar Sin.
Ya kara da cewa, Sinawa suna sha’awar koyon abubuwa kuma suna son aiwatar da abun da suka koya a aikace, domin gabatar da sabbin ilimi da sakamako na zahiri da ci gaba da kirkiro abubuwa. Ya ce wannan ra’ayi ne da ya darsu cikin al’adar kasar cikin dubban shekaru, kuma yanzu mutanen Sin na karkata ne ga mayar da hankali kan kimiyya da fasaha da bangaren injiniya da lissafi.
Ya kuma bayyana cewa, ginshikin samun nasara a sabon zamani ya dogara ne da kimiyya da fasaha. Kuma gwamnatin Sin na yayata bukatar gina al’umma mai koyon abubuwa, tare da goyon bayan kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da tubalin kimiyya kamar lissafi. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp