Rundunar ‘yansandan jihar Inugu ta sha alwashin gaggauta yin bincike kan mutuwar wasu mutane shida tare da wani ango a jihar Inugu.
Saboda haka ne ma jami’an tsaro suka dukufa domin gano, yadda aka yi wannan al’amari ya faru.
- Kudin Da NNPC Ke Kashewa A Tallafin Mai Ya Wuce Kima – Hamid Ali
- Gidauniyar Malam Inuwa Da Kokarinta Na Ilmantar Da Mutanen Karkara Da Rugage
Lamarin dai ya faru ne a wani kauye mai suna Akutara da ke karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Inugu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, DSP Daniel Ndukwe ne ya bayyana haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a garin an Inugu.
Ya ce, ‘yansanda sun samu wannan labarin na mutuwar mutum shida da kuma kwantar da wasu mutum takwas a asibiti.
Binciken da aka fara, ya nuna cewa daya daga cikin wadanda suka mumun mai suna Obinna Dike ya dawo daga bikin aurensa ne da aka yi a garin Obollo-Eke da ke karamar hukumar Udenu, ranar 26, ga watan Agusta, 2022.
Dike ya je wajen auren nasa tare da ‘yan uwansa da kuma wasu makota da wannan abu ya rutsa da su, wadanda suka je bikin auren.
An wayi gari, an ga sun mutu a dakin da aka sauke su, kuma dakin da suke ciki an kulle shi. Dukkansu an same su a sume, bakinsu na kumfa, daga nan aka garzaya da su asibiti.
A asibitin aka tabbatar da cewa, dukkansu sun mutu, saboda haka bayan tabbatar da mutuwarsu sai aka kai gawar ta su mutuware.
Yanzu haka dai kwamishina ‘yansanda, na jihar Ahmed Ammani ya umarci a yi cikakken bincike kan wannan lamari, sannan kuma, ya jajanta wa iyalan wadanda wannan abu ya shafa.