Rahotanni sun bayyana cewa, annobar cutar murar tsintsaye (Bird flu), ta bazu a Jihohin Filato da Katsina.
A makwanni biyu da suka gabata ne, Gwamnatin Tarayya ta ankarar da masu kiwo, musamman na tsintsaye da ofis-ofis na rassan likitocin dabbobi na kasar nan kan barkewar wannan cuta a Jihar Kano.
- Badakala: Bankin Duniya Ya Kakaba Wa Kamfanoni 2 A Nijeriya Takunkumi
- NPA Da Kamfanin NLNG Za Su Kulla Hadakar Fitar Da Iskar Gas Ketare
A ranar 23 ga watan Janairun 2025 ne, aka samu rahoton bullar cutar a yankin Farin Gada da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa.
Daraktan duba lafiyar dabbobi na Jihar Filato, Dakta Shase’et Sipak Dawat, a cikin sanarwar da ya fitar a jihar ya bayyana cewa, an samu barkewar annobar murar ce ga kajin gidan gona a wani wajen kiwata su, inda cutar ta harbi tsintsaye sama da 3,000.
Dakta Dawat, ya nuna damuwarsa kan yadda mai kiwon tsintsayen da cutar ta shafa ya sayar da su kafin likitocin dabbobi daga Ma’aikatar Aikin Noma da Raya Karkara su ziyarci wajen kiwon nasa, domin daukar matakan da suka dace.
“Wannan dalili ne yasa, ake shawartar masu kiwon kajin gidan gonar da su kasance masu sanya idanu tare da tabbatar da tsaftace guraren da suke yin kiwon nasu, domin bai wa tsintsayen da suke kiwatawa kariyar da ta kamata”, in ji Dawat.
Bugu da kari, a Jihar Katsina kuwa, wani jami’in kula da lafiyar dabbobi a shiyyar Karamar Hukumar Malumfashi, Dakta Yau Ishaku; a wani sako da ya isar ga masu kiwon tsintsaye a jihar, ya bayyana bullar annonar a jihar, wanda ya sanar da cewa, ta bulla ne a cikin kwana biyu da suka wuce, kafin samun bullar ta a Jihar Filato.
“Cutar ta bulla ne a Jihar Katsina, a ranar 21 ga watan Janairun 2025, sannan kuma yana da muhimmanci ga daukacin masu kiwon tsitsayen a Kananan Hukumomin Malumfashi, Kafur da Kankara da ke karkashin ofishin shiyya a Karamar Hukumar Malumfashi, da su tabbatar da sun kiyaye wajen daukar matakai, domin kare guraren da suke aiwatar da kiwonsu daga kutsawar wannan annona.”
Ya kara da cewa, ya zama wajibi ga masu kiwon da su rika hana barin mutane suna shiga guraren da suka killace, domin kiwon nasu.
Dakta Yau, ya kuma shawarci masu kiwon da su tabbatar da suna tsaftace kayan da suke amfani da su wajen ciyar da tsitsayen da suke kiwatawa, domin kare su daga kamuwa da cututtuka.