Shahararren tararon damben bodin na duniya ajin masu nauyi, Tyson Fury ya bai wa Anthony Joshua damar fadan neman kambun damben duniya a karshen wannan shekarar da take shirin karewa.
Fury, mai shekaru 34, ya na neman wanda za su fafata da shi bayan da abokin hamayyarsa Oleksandr Usyk, ya nuna cewa ba zai koma fagen dambe ba har sai zuwa shekarar 2023 mai zuwa.
Joshua dan asalin Nijeriya, wanda Usyk dan qasar Ukraine, ya doke shi a Saudi Arabia cikin watan da ya gabata, ya karbi qalubalen Fury, ya na mai cewa tabbas watan Disamba ya yi masa daidai.
Fury ya shaida wa Joshua cewa, ya na sane da cewa bashi da kambu ko guda 1 yanzu haka a hannunsa bayan doke shi a watan jiya, dalili kenan da ya qalubalance shi kan fadan domin ya zama dama gareshi ta samun sabon kambu.