• Leadership Hausa
Tuesday, March 21, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Muhimmiyar Abokiyar Hulda Ce Da Afrika Za Ta Iya Hada Hannu Da Ita Wajen Yaki Da Yunwa

by CMG Hausa
6 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Kasar Sin Muhimmiyar Abokiyar Hulda Ce Da Afrika Za Ta Iya Hada Hannu Da Ita Wajen Yaki Da Yunwa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wani masanin tattalin arziki na kasar Rwanda Egide Karuranga, ya bayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin muhimman kasashen duniya da kasashen Afrika za ta iya hada hannu da su, wajen yaki da karancin abinci a nahiyar, saboda gogewar da take da shi da tarin fasahohin aikin gona.

Masanin na kasar Rwanda ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gefen taron raya muhalli na Africa Green Revolution da aka kammala a Kigali, babban birnin kasar.

  • Ranar Malaman Kasar Sin: Menene Sirrin Ci Gaban Kasar Sin?

A cewarsa, Afrika na iya koyon dabarun kasar Sin bisa la’akari da yadda Sin din ta yi nasarar yaki da yunwa da tamowa.
Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta iya zuba jari a bangaren samar da ruwa da noman rani, yana mai bayyana su a matsayin tubalin dake bukatar mayar da hankali kansu fiye da komai a tsarin matakan raya tattalin arziki.

Ya ce misali, Afrika na gwagwarmaya da noman rani da samun amfanin gona, amma Sin tana da matukar gogewa a wannan fanni.

Haka kuma, akwai kirkire-kirkiren fasahohin aikin gona da tuni aka gwada, aka aiwatar tare da ganin nasararsu a kasar Sin, wadanda za a iya amfani da su a nahiyar Afrika. (Fa’iza Mustapha)

Labarai Masu Nasaba

Sin Ta Fitar Da Rahoto Game Da Halin Dimokuradiyya A Amurka A Shekarar 2022

An Kaddamar Da Shirin Bidiyon “Bayanin Magabata Da Xi Jinping Ke So” Na 2 Da Harshen Rashanci 

ShareTweetSendShare
Previous Post

Anthony Joshua Zai Fafata Da Tyson Fury A Disamba

Next Post

Mutane 20 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Oyo

Related

Sin Ta Fitar Da Rahoto Game Da Halin Dimokuradiyya A Amurka A Shekarar 2022
Daga Birnin Sin

43 mins ago
An Kaddamar Da Shirin Bidiyon “Bayanin Magabata Da Xi Jinping Ke So” Na 2 Da Harshen Rashanci 
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Shirin Bidiyon “Bayanin Magabata Da Xi Jinping Ke So” Na 2 Da Harshen Rashanci 

11 hours ago
Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Rasha Vladimir Putin

Firaministan Kasar Djibouti Ya Mikawa Tawagar Jiyya Ta Kasar Sin Lambar Yabo

13 hours ago
Dangantakar Sin Da Rasha Ta Bayyana “Hanyar Da Ta Dace Ta Cudanya Tsakanin Kasa Da Kasa”
Daga Birnin Sin

Dangantakar Sin Da Rasha Ta Bayyana “Hanyar Da Ta Dace Ta Cudanya Tsakanin Kasa Da Kasa”

14 hours ago
Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Sauran Kasashen Yammacin Duniya Da Su Gaggauta Dage Takunkumin Kan Bangare Daya

15 hours ago
Next Post
Mutane 20 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Oyo

Mutane 20 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Oyo

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Fitar Da Rahoto Game Da Halin Dimokuradiyya A Amurka A Shekarar 2022

Sin Ta Fitar Da Rahoto Game Da Halin Dimokuradiyya A Amurka A Shekarar 2022

March 21, 2023
Jihar Zamfara: Dauda Lawal Dare Na Jam’iyyar PDP Ya Kayar Da Gwamna Matawalle Na APC

Jihar Zamfara: Dauda Lawal Dare Na Jam’iyyar PDP Ya Kayar Da Gwamna Matawalle Na APC

March 21, 2023
An Kaddamar Da Shirin Bidiyon “Bayanin Magabata Da Xi Jinping Ke So” Na 2 Da Harshen Rashanci 

An Kaddamar Da Shirin Bidiyon “Bayanin Magabata Da Xi Jinping Ke So” Na 2 Da Harshen Rashanci 

March 20, 2023
Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Rasha Vladimir Putin

Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Rasha Vladimir Putin

March 20, 2023
Ramadan: Shehu Isma’ila Mai Diwani Ya Buɗe Tafsirin Alƙur’ani A Kaduna

Ramadan: Shehu Isma’ila Mai Diwani Ya Buɗe Tafsirin Alƙur’ani A Kaduna

March 20, 2023
Firaministan Kasar Djibouti Ya Mikawa Tawagar Jiyya Ta Kasar Sin Lambar Yabo

Firaministan Kasar Djibouti Ya Mikawa Tawagar Jiyya Ta Kasar Sin Lambar Yabo

March 20, 2023
Da Dumi-duminsa: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake A Ondo

An Sace Baturen Zabe Akan Hanyarsa Ta Zuwa Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe A Zamfara

March 20, 2023
Dangantakar Sin Da Rasha Ta Bayyana “Hanyar Da Ta Dace Ta Cudanya Tsakanin Kasa Da Kasa”

Dangantakar Sin Da Rasha Ta Bayyana “Hanyar Da Ta Dace Ta Cudanya Tsakanin Kasa Da Kasa”

March 20, 2023
Gwamna Zulum Ya Sake Lashe Zaben Gwamna A Jihar Borno

An Kashe ‘Yansanda 2, Da Dama Sun Samu Raunuka A Wata Arangama Da Sojoji A Taraba

ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci