Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce, jam’iyyar APC ba ta da ‘yan takara a kujerun ‘yan Majalisar Dattawa masu neman wakiltar mazabar Yobe ta Arewa da mazabar Akwa Ibom ta Arewa Maso Yamma.
Wadannan mazabun dai su ne wadanda aka yi ta muhawara a kansu dangane da cewa Sanata Ahmad Lawan da Godswill Akpabio sun nemi zama ‘yan takara amma kura ta tashi.
Babban kwamishina kuma jami’an watsa labarai da ilmantar da masu zabe, Festus Okoye shi ne ya shaida hakan jiya a lokacin da ke magana ta cikin wani shirin gidan talabijin din Channels mai suna ‘Siyasa A Yau’ ya ce hukumar ba ta amince da kowani mutum cikin biyun a matsayin ‘yan takarar mazabun ba.
Ya ce, “Hukumar ta fayyace komai cikin sashi na 29 subsection 1 na dokar zabe. Hakki ne na jam’iyya ta mika sunan jerin sunayen ‘yan takarar da suka samu nasara a zabukan cikin gida da aka gudanar ta sahihi kuma ingataccen hanya ga hukumar zabe ta INEC.
“Wadannan mazabun guda biyu. Sun tura wa INEC sunayen mutane biyu kuma ba mutanen da suka samu nasara ta hanyar gudanar da sahihin zaben fitar da gwani ba ne.
“Kuma ba mu wallafa bayanansu ba, a haka ake har yanzu.”
Okoye ya ce hukumarsu ba za su fito ta je tana rokon APC ko wata jam’iyya da ta tura mata sunan wani dan takara da ya lashe zaben ta sahihin zaben cikin gida ba.
“Idan jam’iyya ba ta aiko mana da sunan wani dan takara da ya samu nasara ta sahihin zaben fitar da gwani ba, matsalar da ke akwai shine ‘ita wannan jam’iyyar’ ba ta da ‘yan takara a mazabun da hakan ya faru, kuma haka doka ta fayyace.”
Ya kara da cewa sunayen Lawan da Akpabio ne APC ta aike cikin shafin INEC inda ita kuma hukumar ta yi watsi da sunayen tare da kin amincewa da su.
“Matsalar ma shine har zuwa yanzu, APC ba ta da ‘yan takara a wadannan mazabun,” ya ce.
Ya kara da cewa ba aiki ne fitar wa jam’iyyun siyasa ‘yan takara ba, illa iyaka su sanya ido wajen gudanar da zaben fitar da gwani domin tabbatar da cewa wadanda aka tura mata sunayensu su ne suka samu nasara a zabukan cikin gida da aka gudanar ta sahihi kuma ingataccen hanya.