Ɗan takarar jam’iyyar APC, Mukhtar Rabi’u Garki, ya lashe zaɓen cike gurbi na Garki/Babura da aka gudanar a ranar Asabar a jihar Jigawa.
Farfaesa Salisu Ibrahim, jami’in tattara sakamakon zaɓen na INEC, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana a dukkanin mazabu 21 na ƙananan hukumomin Garki da Babura.
- Ɗan Shekaru 15 Ya Kashe Wani Matashi Kan Rikicin Gona A Jigawa
- Daje Na Jam’iyyar APC Ya Lashe Zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Neja
Sakamakon ya nuna cewa APC ta samu ƙuri’u 38,449, yayin da PDP ta samu 13,519, sai NNPP da ta tashi da 2,931.
Da haka, an ayyana Mukhtar Rabi’u Garki na APC a matsayin wanda ya yi nasara kuma ya lashe kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Garki/Babura.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp