Jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a Jihar Enugu, inda ta kwashe kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 17 da kuma kujerun kansiloli 260 da ke faɗin jihar baki ɗaya.
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Enugu (ENSIEC), Farfesa Christian Ngwu, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi bayan kammala tattara sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar, 26 ga Satumba, 2026.
Farfesa Ngwu, wanda shi ne Babban Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓen, ya ayyana ƴan takarar jam’iyyar APC a matsayin waɗanda suka yi nasara a dukkan kujerun shugabancin ƙananan hukumomi da na kansiloli, inda ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta lashe zaɓen a dukkan mazaɓu 260 na jihar.
A cewar shugaban na ENSIEC, an bayyana ƴan takarar na APC a matsayin zaɓaɓɓu ne bayan sun cika dukkan ƙa’idojin da doka ta tanada, tare da samun mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa a yayin zaɓen.
Wannan gagarumar nasara ta bai wa jam’iyyar APC cikakken iko a kan dukkan shugabancin ƙananan hukumomi 17 da mazaɓun siyasa da ke faɗin Jihar Enugu.














