• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

APC Ta Yi Allah Wadai Da Rusau Din Da Abba Ke Yi A Kano

by Sadiq
2 years ago
APC

Jam’iyyar adawa a Jihar Kano wato APC ta yi Allah wadai kan abin da ta bayyana da cewa “kai farmaki ne kan dukiyoyin al’umma” da gwamnatin NNPP karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi a jihar.

A cikin wata sanarwa da mukaddashin shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Hon. Shehu Maigari ya aika wa manema labarai, APC ta ce ”a yau Kano ta kasance abin tausayawa sakamakon halin da jam’iyyar NNPP ta jefa jihar ciki”.

  • Gwamnan Bauchi Ya Dauki Sabbin Ma’aikata 1,683
  • Kotu Ta Dakatar Da EFCC, ICPC, DSS Daga Tsare Sanata Yari

Jam’iyyar ta APC ta zargi NNPP da gwamnatin Abba Gida-Gida da jefa ‘yan kasuwa cikin mawuyacin hali, inda ta ce harkokin kasuwancin Kano sun tsaya cik.

APC ta kuma yi zargin cewa matakin da NNPP ta dauka na rusa wasu wuraren kasuwanci a jihar ya sanya wasu matasa a Kano sun zama barayi, inda ta ce matasan suna yawo da makamai tare da fasa shagunan mutane domin satar kaya.

Haka kuma jam’iyyar adawar ta yi kira ga iyayen yara musamman matasan da ta ce gwamnatin NNPP na amfani da su wajen barnata kayan al’umma, su ja kunnen ‘ya’yan nasu.

LABARAI MASU NASABA

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Ita dai jam’iyyar NNPP tare da Abba Gida-Gida sun sha alwashin kwace wurare da suka ce mallakar al’ummar Kano amma gwamnatin APC ta sayar a lokacin da take kan karagar mulkin jihar.

Kwanaki kalilan bayan rantsar da sabon gwamnan na Kano, Abba Kabir Yusuf ya fara rusa wasu gine-gine a filayen da ya ce na al’ummar Kano ne, a cikinsu har da filin sukuwa da otal din Daula da sansanin alhazan jihar da Babban Filin Idin Kano.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Triumph
Manyan Labarai

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
Manyan Labarai

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Next Post
Za A Gudanar Da Bikin Baje Kolin Cinikayya Na Sin Da Afirka A Birnin Changsha

Za A Gudanar Da Bikin Baje Kolin Cinikayya Na Sin Da Afirka A Birnin Changsha

LABARAI MASU NASABA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.