Arangamar da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan sintiri a Zak da ke karamar hukumar Wase ta jihar Filato ta yi sanadiyyar mutuwar mutum goma sha biyu.
In za a iya tuna wa dai a makon da ya gabata ne, wadansu mutane wadanda ake kyautata zaton cewa, ‘yan bindiga ne suka kashe sojoji bakwai da wani dan sintiri guda a yankin masarautar Bashar.
An bayyana wannan labarin ne, lokacin da kwamitin da majalisar wakilai ta kafa kan wannan matsala, ya ziyarci yankin da wannan abu ya faru.
In dai za a iya tuna wa ‘yan bindiga sun gargadi mutanen wasu kauyuka da su gaggauta barin kauyukan nasu kafin su zo, su yi musu kisan kare-dangi.
Dagacin kauten Kanpani Zurak, Alhaji Dahiru Adamu, da wasau sarakunan da ke Wase sun bayyana cewa, sun samu labarin cewa, kwamitin majalisar wailai ya je domin ya bincika,kisa da kuma garkuwa da mutanen da aka yi a wannan yanki.
Wani mutum da ke zaune a Zak, mai suna Sambo, ya ce, “Wannan abin ya faru ne da misalin karfe 9 na dare, wanda kuma sakamakon wannan arangama aka kashe mutum tara daga cikin ‘yan bindigar sannan kuma mutum uku daga cikin ‘yan sintirin suka mutu.
Sambo ya kara da cewa, “’yan bindigar sun zo a kan babura ne. Nuna kyautata zaton sun fito daga wani daji ne suka nufi Zak.
“Lokacin da al’ummar wannan yankin suka fahimci an rutsa ‘yan bindigar, sai suka yi gaggawar sanar da rundunar ‘Operation Safe da ke Zak wadanda kuma nan da nan suka yi shirin yaki suka fito tare da ‘ya sintiri. Nan fa aka fara dauki ba dadi”.
Wanda kuma rundunar jami’an tsaron suka samu nasarar kashe ‘yan bindigar da kuma tarwatsa wasu, suka afka daji,