Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana cewa yankin Arewa bai dogara da sauran yankunan ƙasar nan ba wajen ci gaban tattalin arziƙinsa ba, yana mai cewa yanzu Arewa tana taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Ya bayyana haka ne a yayin rufe taron Bauchi Investment Summit 2025 da aka gudanar a Cibiyar Taro ta Sir Ahmadu Bello International Conference Centre a Bauchi, inda ya jaddada cewa Arewa ta shafe shekaru tana samar da muhimman albarkatu ga ƙasar.
- HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi
- Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
Gwamnan ya ce yarjejeniyoyin saka jari da aka cimma a taron na kwanaki biyu sun nuna cewa Arewa na tasowa a matsayin cibiyar tattalin arziƙi, musamman ganin yadda masu zuba jari ke nuna ƙwarin gwuiwa ga Jihar Bauchi da maƙwabta.
Bala Mohammed ya ce lokaci ya yi da za a daina dogaro da man fetur daga Kudu, domin yanzu an gano ma’adinan man fetur a Bauchi da wasu jihohin Arewa. Haka kuma, ya bayyana cewa Arewa tana da tarin ma’adinai da arziƙin noma da za su iya haɓaka tattalin arzikin ƙasar.
Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da a sauya tunani, a daina kallon Arewa a matsayin nauyi, a maimakon haka a ɗauke ta a matsayin muhimmiyar abokin haɓaka tattalin arziƙi, domin Arewa tana shirye ta taka cikakkiyar rawa a ci gaban Nijeriya.