A ci gaba kafsa yaki tsakanin Kasar Rasha Da Yukiren, Yukiren din ta sake yin kira ga kasashen duniya da su samar mata da karin kayan yaki domin tunkarar mamayar Rasha.
Shugaba Bolodomyr Zelensky ya shaida wa taron Nato na makon da ya gabata cewa: “Muna bukatar mu karya lagwon makaman Rasha. Muna bukatar karin makamai na zamani.”
Ya ce idan har Yukiren ba ta samu makaman da take bukata ba don kayar da Rasha ba, to shugabannin NATO za su fuskanci yaki a nan gaba da Moscow da kansu.
Kasashe sama da 30 ne suka bai wa kasar Yukiren dinbin kayayakin yaki, sai dai ana tafiyar hawainiya game da manyan makamai, kuma a wasu yankunan sojojin Yukiren ba su da makamai.
Wadanne kasashe ne suka fi ba Yukiren makamai?
Birtaniya ita ce ta biyu yayin da Poland ita ce ta uku a jerin kasashen da ke kashewa Yukiren makudan kudade.
Dangane da kudaden da aka kashe, maimakon alkawuran bayar da kudi da kasashe suka yi, Fadar White House ta ce Amurka ta bayar da tallafin Dala biliyan 6.3 a matsayin taimakon tsaro ga Yukiren tun lokacin da Shugaba Joe Biden ya hau karagar mulki a watan Janairun 2021.
Birtaniya ta ce ta samar da Dala biliyan 1.6 , kuma ta yi alkawarin bayar da karin Dala biliyan 1.2 tun farkon yakin.
Shugaba Zelensky ya nemi karin kudade, kuma ya ce kudaden da kasar ke kashewa kan tsaro a kowanne wata ya kusan Dala biliyan 5.
Wadanne irin makamai ne Yukiren ta ke bukata?
Kwararun sojoji sun ce samun nasara a fagen daga na bukatar manyan makamai, da horo da kayayyakin gyara da sauran tallafi.
“Babu tsarin makami da ya zama harsashi na azurfa,” a cewar Janar Mark Milley, Shugaban Hafsan Hafsoshin Sojojin Amurka.
Duk da haka, ana kyautata zaton na’urorin makamai da dama sun taka muhimmiyar rawa a rikicin ya zuwa yanzu.
Rokoki masu cin dogon zango
Yayin da sojojin Rasha ke ci gaba da luguden wuta a yankunan Yukiren da ke Gabashin kasar, manazarta sun ce Yukiren tana matukar bukatar samar da ingantattun makamai da harsasai don rike manyan yankunanta.
Ya zuwa yanzu, ana tunanin cewa an tura wa kasar makaman roka guda 10 masu cin dogon zango ko kuma suna kan hanya, daga Amurka da Birtaniya da Jamus.
Yukiren ta ce ana bukatar wasu da dama domin dakile dannawar sojojin Rasha.
Makaman yakin na Amurka sun hada da na’urar roka ta M142 ko Himars Kayayyakin da aka ba wa Yukiren a halin yanzu makaman da aka ba Yukiren za su iya cin dogon zango na mil 43.5 wato kilomita 70.
Howitzers
Australia da Canada da kuma Amurka sun tura da karin makamai da ake kira howitzers sama da 100 da kuma alburusai dubu dari 300 zuwa Yukiren.
Kasashen Yamma sun yi tafiyar hawainiya wajen amsa bukatar Yukiren na neman manyan makamai.
A farkon yakin akwai damuwa game da tsokanar Rasha.
‘Yan siyasa kuma sun dauka sojojin Yukiren ba za su kai labari ba.
Bayan dan lokaci wannan tunani ya canza, ko da yake har yanzu akwai tambayoyi game da kudirin Yamma na ci gaba da bai wa Yukiren makamai.
Da farko an mayar da hankali ne kan samar wa Yukiren makamai masu jituwa – wadanda aka horar da su don amfani da su.
Wannan ya hada da tankunan yaki na zamanin tarayyar Sobiet, na’urorin tare makamai ta sama da harsasai.
Amurka da sauran kawayenta sun taimaka wa Turai don neman makaman makamancin haka, amma wadannan tarin makaman sun ragu matuka.
Don haka a yanzu ana son a turawa kasar da karin makamai na zamani na kasashen yamma tare da fatan za su dore a cikin dogon lokaci.
Amma hakan ya kawo karin kalubale.
Tsarin makaman zamani galibi ya fi rikitarwa kuma yana bukatar horo, ba kawai yadda ake sarrafa su ba, amma don kula da su da gyara su.
Makaman lalata tankokin yaki
An turawa Yukiren da makaman lalata tankokin yaki akalla 5,000 da ake kira Nlaw.
Yukiren ta karbi tankokin yaki sama da 230 daga Poland da Jamhuriyar Czech.
Sojojin Yukiren sun shafe shekaru suna amfani da tankokin yaki kirar T-72 kuma suna da kayayyakin gyara da kuma sojoji da suka kware a wannan fanni.
Jiragen yaki marasa matuka
An yi amfani da jiragen sama marasa matuka a yakin Yukiren inda an yi amfani da dama wajan sintirin tsaro da kai hari da kuma jigilar kayayyaki masu nauyi.
Turkiyya ta sayarwa Yukiren da jirgin sama marasa matuka na Bayraktar TB2 a watannin baya-baya nan.
Masu sharhi sun ce jirgin sama mara matuki na Bayraktar TB2 ya yi tasiri sosai wajen kai wa sojojin Rasha hari.
An yi ammanar cewa an yi amfani da su wajen lalata jiragen sama masu saukar ungulu da jiragem ruwan yaki da makamai masu linzami
Na’urar tare makami ta sama
Yukiren ta yi nasarar hana Rasha cikakken ikon mallakar sararin samaniyarta a lokacin rikicin, amma ta yi kira akai-akai da samar mata naurar tare makami ta sama mai inganci.
A cikin kwanaki masu zuwa, ana sa ran Washington za ta sanar da cewa za ta aika NASAMS, na’urar harba makami mai linzami daga sama