• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Asibitin Yariman Bakura Ya Fara Amfana Da Dokar Ta-ɓaci A Sashen Kiwon Lafiyar Zamfara

by Leadership Hausa
1 year ago
asibiti

Asibitin Yariman Bakura da ke Gusau ya fara amfana da dokar ta-ɓaci a sashen kiwon lafiya da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ayyana sakamakon ƙaddamar da aikin gyara, ingantawa da kuma samar da kayan aiki a asibitin ƙwararrun ɗaya tilo mallakar gwamnatin jihar.

An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a ranar Alhamis da ta gabata a asibitin ƙwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura da ke Gusau, babban birnin jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa ingantawar za ta mayar da asibitin zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Zamfara.

A yayin jawabinsa a wurin taron, Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa, gyaran zai inganta tsarin kula da marasa lafiya ta musamman, da ƙara yawan ma’aikatan kiwon lafiya, da kuma inganta tsarin ayyukan, wanda zai haifar da ingantaccen kiwon lafiya.

“Mun zo nan a yau ne domin ƙaddamar da gyare-gyare da kuma samar da kayan aiki na asibitin ƙwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura da ke Gusau. Aikin zai kuma ƙunshi samar da kayan aikin jinya ga asibitin. Wannan aiki dai ya biyo bayan ayyana dokar ta-ɓaci ne a fannin kiwon lafiyar jihar, bayan na ilimi.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

“Wannan babban ƙalubale ne da muka gada a wannan fanni lokacin da muka karɓi ragamar mulkin jihar.

“Asibitin na cikin mawuyacin hali duk da irin rawar da yake takawa wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga mazauna da baƙi a jihar bakiɗaya. Yawancin kayan aikinsa sun lalace, wanda hakan ke nuna buƙatar kulawar gaggawa. Bugu da ƙari, asibitin ba shi da isassun kayan aikin ɗakin gwaje-gwaje, wanda ke kawo cikas ga ma’aikatan wajen aiwatar da muhimman hanyoyin gano cututtuka yadda ya kamata.

asibiti

“Manufarmu ba wai don kare lafiya da jin daɗin mazauna jihar da ma’aikatan kiwon lafiya ba ne kawai, sai dai har da magancewa da shawo kan cututtukan da ke yaɗuwa da kuma waɗanda ba sa yaɗuwa.

“Muna da niyyar samar da cikakkiyar tsarin kula da lafiya wanda zai ƙunshi nau’ikan ayyuka masu muhimmanci, gami da samar da magunguna masu muhimmanci, matakan rigakafi, sake fasalin manufofin kiwon lafiya, aiwatar da ƙa’idoji kan tsaftar ruwa da ƙa’idojin tsabtar muhalli, kula da yanayin kiwon lafiya, shirye-shiryen rigakafi, kula da lafiyar mata masu juna biyu, inganta tsarin abinci mai gina jiki gami da ƙarfafa tsarin ba da gudummawar kuɗaɗen kula da lafiya.

“Kamar yadda Asibitin ƙwararru na Yariman Bakura ya kasance shi ne kaɗai cibiyar kula da lafiya mallakar jihar, akwai buƙatar ya samar da kulawa ta musamman da suka shafi haɗaɗɗun matakan jiyya, tare da ba da horo ga ƙananan likitoci da samar da yanayi mai kyau ga ƙwararrun kiwon lafiya da ke gudanar da bincike a fannonin kiwon lafiya daban-daban. Ya zama wajibi mu tabbatar da sake fasalin asibitin. Mun yi niyyar mayar da Yariman Bakura asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Zamfara da zarar an fara Kwalejin Kimiyyar Lafiya.

asibiti

“Abubuwan da za a aiwatar da gyaran a kan su za su haɗa da sabbin gine-gine, faɗaɗawa da inganta gine-ginen da ake da su, gyara gine-ginen da ake da su, da kammala rukunin ginin likitoci, da bunƙasa ɗakin gwaje-gwaje. Haɓaka kayayyakin aiki da inganta cikakken tsarin Kula da Bayanan Asibiti.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka
Kiwon Lafiya

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha
Kiwon Lafiya

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025
Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
Kiwon Lafiya

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa

October 11, 2025
Next Post
Yadda Aka Yi Wa Finidi George Kora Da Hali Daga Aikin Kocin Super Eagles

Yadda Aka Yi Wa Finidi George Kora Da Hali Daga Aikin Kocin Super Eagles

LABARAI MASU NASABA

Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025
An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

November 7, 2025

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025
Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.