Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba.
Amorim ya ce a ranar Laraba yana jin ƙungiyarsa za ta fi kyau da Rashford a ciki, amma ɗan wasan bai cika ƙa’idojin da ya buƙata ba, wakilan Rashford sun gana da wasu manyan ƙungiyoyin Turai a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a ƙoƙarinsu na ganin ya bar Manchester.
- Mece Ce Matsalar Manchester United?
- AC Milan Ta Kammala Ɗaukar Kyle Walker Daga Manchester City A Matsayin Aro
Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa har yanzu ba a yanke shawarar makomar Rashford ba, har yanzu Manchester ba ta bayar da damar sayen Rashford ba amma kuma akwai yiwuwar ta bari ya tafi a matsayin aro, Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan na Ingila, Rashford yana ɗaya daga cikin manyan masu karɓar albashi a United, tare da albashi sama da £300,000 a mako.