Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
A yau shafin namu zai koya muku yadda za ku hada Sabaya da kanku:
A yau amfani da sabaya ya zama ruwan dare yayin da mata suke ta tambayar ya za su hada sabaya, wasu kuma suna ta korafi sun saya amma bai musu aiki ba duk da cewa akwai abubuwan da suke iya hana sabaya aiki amma mafi yawa rashin ingancin sabayar ne.
To yau zan share muku hawayenku na gaya muku yadda za ku hada sabaya mai inganci cikin sauki, in dai Sabaya kuke bukata mai kyau da inganci to damuwarku ta zo karshe da izinin Allah.
Kayan hadi:
”Yayan Hulba (gongoni 2, Aya (gongoni 3), Ridi (gongoni 1)
Ga kuma Yadda za ku hada:
Wadannan kayan hadin ku soya su duka amma sama-sama sai ku bar su su huce sanna ku daka ko ku nika ku tankade.
Yadda ake amfani da ita:
Za ku dinga diban cokali 2 ko 3 kusa madara cokali 2 kusa ruwan zafi ku gauraya ku shanye, sannan ana sha ne safe da rana da dare na tsawon sati 3 ko 4. Kazalika ku nemi garin hulba ku debi kadan kusa ruwan zafi ku gauraya sai ku sanya wani abu ku dinga dandanar ruwan kuna gasa shi, sannan ku samu man hulba da man zaitun da man ridi ku gauraya bayan kun gasa su sai ku wanke ku shafa wannan mai.
Dan Allah Hajiya ki yi wannan abin na sati 3 ko 4 ki gani tabbas za ki sa min albarka.