Sanata Ali Ndume ya shawarci gwamnatin tarayya ta zabtare albashin ‘yan majalisa da kashi 50 cikin 100 domin biyan malaman jami’o’i da ke yajin aiki kuɗaɗensu.
BBC ta rawaito cewa, Sanata Ndume da ke wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattijai ya shaida hakan ne a birnin Maiduguri lokacin wani taro.
- Da Dumi-Dumi: ASUU Ta Musanta Shirin Sake Shiga Yajin Aiki
- Yau Litinin Kungiyar ASUU Za Ta Yi Taro Kan Shiga Sabon Yajin Aiki
Jaridun Nijeriya sun rawaito sanatan na cewa wannan abu ne da ya shafi kasa baki ɗaya, kuma dole a wasu lokutan a ɗau matakan ceto ‘yan kasa da ilimi.
Kiran da sanatan ya yi na zuwa ne adaida lokacin da malaman jami’i’oi ke korafin cewa rabin albashinsu aka basu bayan sun janye yajin aiki.
Dan majalisar dai na cewa lokaci ya yi da ya kamata a shawo kan matsalolin da ke durkusar da fanin ilimi a Nijeriya.
A watan Oktoban da ya gabata ne, ASUU ta janye yajin aiki da ta shafe wata takwas tana yi ba tare da ta samu biyan bukatunta daga wajen gwamnatin tarayya ba.