Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU), ta kawo karshen taronta na kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da kudirinta na sake shiga wani sabon yajin aiki.
Sai dai kungiyar ta yi Allah-wadai da yunkurin gwamnatin tarayya na mayar da malaman jami’o’i zaman banza ta hanyar biyansu albashinkwanaki 18.
- An Rufe Kasuwar Dutsen Alhaji Saboda Kazanta A Abuja
- Shugaban Kasar Sin Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Cikar Kungiyar INBAR Shekaru 25 Da Kafuwa
A wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a ranar Talata, bayan kammala taron NEC, shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa malaman jami’o’i hazikai ne ba gama-garin ma’aikata ba.
Ya ce kungiyar ta dakatar da yajin aikin na watanni takwas a ranar 14 ga Oktoba, 2022 bisa bin umarnin kotun masana’antu ta kasa da kuma la’akari da kokarin tsoma bakin ‘yan Nijeriya masu kishin kasa, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila.
Osodeke ya yi nuni da cewa, matakin da kungiyar ta dauka na nuna amincewa da bangaren shari’a da sauran cibiyoyi da ma’aikatun gwamnati a ko da yaushe su sanya maslahar kasa gaba da duk wani abu.
Shugaban ASUU, ya koka da yadda gwamnati ta mayar da martani ta hanyar biyansu kudin kwanaki 18 a matsayin albashin malaman jami’o’i na watan Oktoba 2022.
Ya ce, “Wannan mun yi imanin, a matsayinmu na kungiya masu tunani, ’yan boko, da masu kishin kasa, ba wai kawai za ta taimaka wajen warware rikicin cikin ruwan sanyi ba, har ma zai kafa hanyar samar da alakar masana’antu tsakanin gwamnati da ma’aikatan Nijeriya baki daya.
“Abin takaici, martanin da gwamnati ta mayar kan yadda ASUU ta nuna amana shi ne biyanmu kudin tsawon kwanaki goma sha takwas a matsayin albashin malaman jami’o’i na Oktoba 2022 ta yadda ake bayyana su a matsayin ma’aikata da ake biyansu a kullum!
“Wannan ba wai kawai rugujewa ba ne, amma ya saba wa duk wasu sanannun ka’idojin aiki a kowace kwangilar aiki ga masana a duniya.
“A taron gaggawa na kungiyar ASUU ta kasa (NEC), wanda aka gudanar a ranar Litinin, 7 ga watan Nuwamba, 2022, kungiyar ta tattauna kan abubuwan da suka faru tun bayan dakatar da yajin aikin.
“NEC ta lura da takaicin cewa biyan malaman jami’o’i, kamar ma’aikatan wucin gadi, ba a taba yin irinsa ba a tarihin dangantakar da ke tsakanin jami’o’i, don haka mun yi Allah-wadai da wannan yunkuri na mayar da malaman Nijeriya kamar sauran ma’aikata.
“NEC ta yaba wa kungiyar ASUU bisa jajircewa da suka yi wajen fuskantar wahalhalu daga wasu jiga-jigan masu fada a ji.”
Don haka kungiyar ASUU ta yi kira da a fahimci daliban Nijeriya, iyaye da sauran daidaikun mutane da kungiyoyin da abin ya shafa, a yayin da kungiyar ke ci gaba da bin diddigin wannan rikici da za a iya kaucewa daga doron kasa ba tare da tauye muradun jin dadin masanan Najeriya ba.