Kungiyar malaman jami’o’i t kasa (ASUU), ta yi kira da gwamnatin tarayya da ta mutunta tare da aiwatar da yarjejeniyar da kungiyar ta shiga da gwamnati.
Ko’odinetan ASUU mai kula da shiyyar Kano, Abdulqadir Muhammad ya bayyana haka a wani taron manema labarai a karshen taronsu na shiyya da aka yi ranar Laraba a Kano.
- Cire Kashi 40 Na Kudin Shigar Jami’o’i Zai Kassara Su – ASUU
- Rashin Cika Alkawari: ASUU Na Gangamin Shiga Wani Sabon Yajin Aiki
Ya ce batutuwan sun hada da sake tattaunawa kan batun yarjejeniyar Gwamnatin Tarayya da Kungiyar ASUU ta shekarar 2009, da aka cimma a lokacin da farashin dalar Amurka ya kai N146 sabanin N1,900 a yanzu.
Muhammad ya ce, farashin canji ya zamewa albashinsu da kashi 90 cikin 100.
Ya koka kan yadda gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan daftarin yarjejeniyar da aka cimma da kungiyar bayan samar kafa sababbin shugabannin da suka jagorancin kwamitin sulhu da kungiyar.