• English
  • Business News
Monday, October 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ASUU Ta Fara Gangamin Shiga Yajin Aiki Yayin Da Gwamnatin Tarayya Ta Kasa Cika Alkawari

by Idris Aliyu Daudawa
10 months ago
in Ilimi, Kasashen Ketare
0
ASUU Ta Fara Gangamin Shiga Yajin Aiki Yayin Da Gwamnatin Tarayya Ta Kasa Cika Alkawari
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Da akwai alamun jami’oi za su fara wani yajin aikin da za s a al’amuran koyarwa su tsaya, yayin da gwamnatin tarayya ta kasa cika alkawarin yarjejeniyar da ta sa hannu da kungiyar Malaman jami’oi ta kasa (ASUU).

Jaridar Guardian ta bada rahoton cewa kungiyar ta damu kwarai kan rashin cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi da ita, na samar da Naira bilyan 200 kowace shekara wanda aka yi 2009 kudaden da za bunkasa jami’oin Nijeriya.

  • Sin Da Amurka Sun Tsawaita Yarjejeniyar Hadin Gwiwa A Fannin Raya Kimiyya Da Fasaha Da Karin Shekaru 5
  • Bankin Duniya Da Hukumar Lamuni Ke Yi Wa Tsarin Ilimin Nijeriya Zagon-kasa – ASUU

Babban jami’in kungiyar da baya son a ambaci sunansa, ya bayyana cewa kungiyar ta shiryawa tafiya yajin aikin, muddin dai gwamnati ta ki sakin kudin saboda ayyukan da ake yi masu muhimmanci da suke karkashin kungiyar, shirye suke su fara yajin aiki idan har Shugaban kasa bai sa an bada kudaden ba.

Wata majiya tace matakin na, ASUU da har yanzu ba’a bayyana shi ba, ya tsaya kan rashin cika alkawarin da gwamnati ta yi na cika alkawarin da tayi tare da kungiyar a shekarar 2009 kan tsarin bukatunsu.Tsarin da aka dauka a matsayin mai canza al’amura wajen sake farfadowa da bunkasa abubuwan more rayuwa da za su taimakawa bunkasar ilimi a Jami’oin Nijeriya.

Majiyar ta ce shi shirin tafiya yajin aikin da za a yi ya dogara ne kan samun matsaya wadda ake sa ran cimmawa bayan taron da za a yi  na kwamitin zartarwa nan gaba bada dadewa ba.

Labarai Masu Nasaba

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

A wani ci gaban da aka samu wani babban kusa, na cibiyar kulawa da ayyuka ta jami’ar Jos Dr. Tunde Olagunjembi, wanda shi ne babban mai bincike ne, daga Jami’ar har ila yau kuma Malamin, ya ba Shugaban kasa shawarar kada ya yi watsi da  tsarin da aka fara wanda an yi shi ne, domin samar da kudade ga Jami’oin gwamnati saboda ci gabansu. Tsarin da aka fara an kirkiro shi ne domin a samu yin gyara kan abubuwan more rayuwa da suka lalace da kuma samar da kayan koyarwa a manyan makarantu.

Olagunjembi ya yi kira da Shugaban kasa ya ci gaba da tsarin da aka fara domin samun ci gaban yadda ake tafiyar da ilimin Jami’oi.

Ya yi kira da Shugaban kasa da kada ya bata lokaci ya amince saboda ci gaba na yin ayyukan, a makarantu da suke a karkashin tsarin.

Ya lashi takobin al’ummar Jami’a da kungiyar ASUU sun kosa da ganin yadda za a ci gaba da ayyukan a karkashin wannan mulkin.

Babban mai fada aji a Jami’a ya kara bayyana cewa samun dorewar karatu a makarantu hakan na faruwa ne sanadiyar sadaukar da kan da ‘yan kungiyar ta ASUU suka yi wadanda suka yanke shawarar za su ba Shugaban kasa lokaci domin ya samu damar tsai da hankalinsa kan ayyukan dake gabansa.

Sai dai kuma duk da hakan ya ja kunne cewar ruwa ya kusa karewa dan Kada,kamata ya yi Shugaban kasa ya dauki matakan da suka kamata wajen samar da kudade  don ci gaban ayyukan da aka fara.

Kamar yadda yace gabatar da, fara amfani samar da kudade saboda a samu aiwatar da tsarin yin ayyuka, hakan ta yiyu ne saboda yarjejeniyar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU, abin ya ta’allaka ne saboda ayi amfani da shawarwarin kwamitin ya bayar, domin ayi maganin matsalolin da ake fuskanta a manyan makarantu/ Jami’oin Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Jami'a
ShareTweetSendShare
Previous Post

Adadin Hatsin Da Kasar Sin Ta Samu A Bana Ya Haura Tan Miliyan 700 

Next Post

Nijeriya Za Ta Shiga Cikin Manyan Kasashe Masu Fitar Da Amfanin Gona A 2025 – Tinubu

Related

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya
Ilimi

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya

12 hours ago
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?
Kasashen Ketare

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

1 day ago
Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet
Ilimi

Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet

2 days ago
Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa?
Kasashen Ketare

Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa?

1 week ago
Ilimin Fasaha Shi Ne Tafarkin Cire Nijeriya Daga Kangin Fatara – NBTE
Ilimi

Ilimin Fasaha Shi Ne Tafarkin Cire Nijeriya Daga Kangin Fatara – NBTE

1 week ago
Birtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa
Kasashen Ketare

Birtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa

2 weeks ago
Next Post
Nijeriya Za Ta Shiga Cikin Manyan Kasashe Masu Fitar Da Amfanin Gona A 2025 – Tinubu

Nijeriya Za Ta Shiga Cikin Manyan Kasashe Masu Fitar Da Amfanin Gona A 2025 – Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu

Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu

October 6, 2025
Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara

Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara

October 5, 2025
Kotu Ta Kori Buƙatar Ministan Tinubu Na Hana Fitar Da Takardun Karatunsa

Kotu Ta Kori Buƙatar Ministan Tinubu Na Hana Fitar Da Takardun Karatunsa

October 5, 2025
CMG Zai Watsa Shirin Nishadantarwa Na Murnar Bikin Zhongqiu Gobe Da Dare

CMG Zai Watsa Shirin Nishadantarwa Na Murnar Bikin Zhongqiu Gobe Da Dare

October 5, 2025
Nijeriya Ta Zamo Ƙasa Mafi Ƙarancin Tsammanin Tsawon Rayuwa A Duniya

Nijeriya Ta Zamo Ƙasa Mafi Ƙarancin Tsammanin Tsawon Rayuwa A Duniya

October 5, 2025
Yawan Mutanen Da Suka Yi Zirga-zirga A Rabin Farkon Hutun Bikin Kafuwar PRC Da Bikin Zhongqiu Ya Kai Biliyan 1 Da Miliyan 243

Yawan Mutanen Da Suka Yi Zirga-zirga A Rabin Farkon Hutun Bikin Kafuwar PRC Da Bikin Zhongqiu Ya Kai Biliyan 1 Da Miliyan 243

October 5, 2025
NUJ Ta Yi Maraba Da Sakin Ƴan Jaridar Da DSS Ta Kama A Jana’izar Mahaifiyar Shugaban APC

NUJ Ta Yi Maraba Da Sakin Ƴan Jaridar Da DSS Ta Kama A Jana’izar Mahaifiyar Shugaban APC

October 5, 2025
Kamfanin Sin Ya Kaddamar Da Ginin Katafaren Wurin Shakatawa Na Zamani A Ghana

Kamfanin Sin Ya Kaddamar Da Ginin Katafaren Wurin Shakatawa Na Zamani A Ghana

October 5, 2025
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya

October 5, 2025
Za A Gudanar Da Taron Motoci Masu Amfani Da Fasahohin Zamani Na Duniya Na Shekarar 2025 A Beijing

Za A Gudanar Da Taron Motoci Masu Amfani Da Fasahohin Zamani Na Duniya Na Shekarar 2025 A Beijing

October 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.