Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU), ta fara yajin aiki a faɗin Nijeriya saboda rashin biyan mambobinta albashin watan Yunin 2025.
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya tabbatar da haka a ranar Litinin a birnin Abuja.
- ADC: Tinubu Na Yunƙurin Raba Kawunan Masu Haɗaka Kafin Zaɓen 2027
- Nijeriya Ba Ta Da Sha’awar Yin Gwajin Makamin Nukiliya — Shettima
Ya ce wannan mataki yayi daidai da dokar Majalisar Zartarwa ta ASUU ta yanke (NEC), inda ta umarci mambobinta da su daina aiki idan ba a biya su albashi tsawon kwanaki uku da yadda aka saba biyansu
Jami’o’i da dama kamar su Jami’ar Jos da Jami’ar Abuja sun fara yajin aikin tuntuni.
Farfesa Piwuna, ya bayyana cewa tun da aka sauya tsarin biyan albashi daga IPPIS zuwa GIFMIS, malaman jami’o’i ke fama da jinkirin biyan albashi, inda wasu ke jira na tsawon sati ko fiye kafin su samu albashin da ba ya wadatar da su.
“Wannan yajin aiki ba wata sabuwar tattaunawa ba ce,” in ji shi.
“Abin da muke yi kawai martani ne ga halin ƙunci da mambobinmu ke ciki. Ofishin Akanta-Janar na ƙasa ne ke jinkirta biyan albashin da gangan.”
ASUU ta ce ta riga ta gana da hukumomin gwamnati don bayyana matsalolinta, amma ba a ɗauki mataki ba.
Farfesa Piwuna, ya kuma ƙara da cewa har yanzu malaman jami’a na bin gwamnati Naira biliyan 10 daga cikin Naira biliyan 50 da za a biya su a matsayin haƙƙoƙinsu (Earned Academic Allowances – EAA).
Ya gargaɗi gwamnati cewa duk wata jami’a da ba a biya malamanta albashi ba, za ta ci gaba da yajin aiki har sai an warware matsalar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp