Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas, yana mai cewa hakan siyasa ce tsantsa kuma ɓaga dimokuraɗiyya.
Atiku, cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana matakin a matsayin wata maƙarƙashiya ta siyasa da aka yi da mugun nufi.
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [11]
- Dabarun Kasar Sin Na Iya Kawo Karshen Yunwa A Duniya
Ya zargi Shugaba Tinubu da haddasa rikicin da ke faruwa a Jihar Ribas, ko dai ta hanyar goyon baya ko kuma ƙin ɗaukar matakin daƙile rikicin.
A cewar Atiku, idan an lalata kadarorin gwamnatin tarayya a jihar, to Shugaban Ƙasa ne ya kamata ya ɗauki alhakin hakan, ba wai a azabtar da al’ummar Ribas da dokar ta-ɓaci ba.
“Ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas siyasa ce kawai, ba don amfanin jama’a ba. Tinubu na da hannu a rikicin kuma ya kasa ɗaukar matakin da ya kamata. Ƙin ɗaukar matakin da ya yi abin kunya ne,” in ji Atiku.
Ya ƙara da cewa rikicin da ke faruwa a yankin Neja Delta a ƙarƙashin shugabancin Tinubu ya rusa zaman lafiyan da aka samu a zamanin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua.
Atiku ya jaddada cewa wannan ba batun tsaro ba ne, illa dai wata hanyar wasa da siyasa tsakanin masu goyon bayan Tinubu da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara.
Ya buƙaci ‘yan Nijeriya su yi Allah-wadai da wannan mataki da ya kira hari kan dimokuraɗiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp