Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi tir da harin da aka kai wa magoya bayan jam’iyyar PDP a taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a jihar Kaduna ranar Litinin.
Atiku, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na twitter, ya kuma yi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya yi kira ga dukkan bangarorin da su kira magoya bayansu su bayar da umarnin an tabbatar da cewa an gudanar da yakin neman zabe cikin lumana.
- Na Amince Zan Goyi Bayan Takarar Atiku Abubakar —Wike
- Atiku Ya Karbi Mutane Dubu 25 Da Suka Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP A Bauchi
Ya ce, “Yanzun nan na samu rahoton kai hari kan magoya bayan PDP da wasu ‘yan daba suka yi a gangamin yakin neman zaben PDP da ke gudana a jihar Kaduna. Wannan bai dace da tsarin dimokuradiyya ba kuma ya sabawa yarjejeniyar zaman lafiya da duk bangarori suka sanya hannu a ‘yan makonnin da suka gabata.
“Ina kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya yi kira ga dukkan jam’iyyu da su kira magoya bayansu da su ba su umarni da kuma tabbatar da cewa an gudanar da yakin neman zabe cikin ‘yanci, adalci da tsaro. – AA,” in ji shi.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Lahadin da ta gabata ne jam’iyyar PDP ta tayar da kayar-baya kan wani shiri da wadanda ta kira masu adawa da dimokuradiyya suka yi na haifar da rikici da hargitsa taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a Kaduna.