Jami’in ilimi yana da gudunmawar da zai rika bada wa ta ɓangaren gyara yaddagaban dalibai da makarantu za su kasance.
Don haka muhimman abubuwan da ake sa ran gani daga jami’in ilimi yana da su sun hada da ya san yadda zai riƙa yin hulɗa da al’umma, saboda ya samu damar bada shawarwari, da kuma abinda ake sa ran zai iya faruwa ko zuwa, kamar yadda ya dace, yana da masaniyar yadda za a tafiyar da jagoranci, domin alƙiblar makaranta ta zama mai kyau, ya kuma zama mai basirar kasancewa yana cikin shirin amaganin duk wata matsalar data shafi ilimi wadda ka iya tasowa.
- Tinubu Ya Buƙaci A Mayar Wa BUK Filin Rimin Zakara Da Ake Taƙaddama A Kai
- Haƙar Ma’adanai Na Sa Yara Ficewa Daga Makaranta A Jos
Su kasance lalle suna sha’awar da kaunar duk wani lamarin da ke da alaka da ilimi, su kuma kasance suna da wayoi, basira, ko kwarewar da za su iya jan hankalin wasu.
Jami’in ilimi akwai bukatar su kasance suna saurarar ra’ayin kowa su kuma rika bayyana abinda suke nufi da yadda suka fahimci shi lamarin da ake magana kan shi,ba domin komai ba sai saboda daga karshe ‘yan makaranta ya zama sun fahimci ko gane duk abubuwan da ake koya masu.
Yadda jami’in ilin iimi zai yi aiki da Iyaye da kuma sauran al’umma
Jami’in ilimi kwararre wanda yake aiki a bangaren ilimi shi ne kuma ke da alhakin wajen tafiyar da lamurran ilimi da suka shafi tsare- tsare da manufofin ilimi, suna tafiya kamar yadda ya dace. Ɗaya daga cikin manufofinsa da ke da amfani ita ce yin aiki kafada- kafada da Iyaye da kuma sauarn mabobin al’umma da kuma tabbatar ana tafiya tare wajen lamarin daya shafi ilimin ‘ya’yansu.
Irin hakan ya kamata ya hada masu da shirya tarurruka, tarurrukan horarwa, domin a samar da labaran da suke da alaka da ba Iyaye shawara,kai har ma da hadin kai kungiyoyin al’umma, da hukumomi,domin samar da wata da wasu hanyoyin da za su taimakawa dalibai.
Babban burin jami’in ilimi shi ne ya samu damar taimakawa domin samun sakamako mai inganci ga dalibai, iyalai, da kuma al’umma, sai kuma samar da lamarin dai rika taimakawa kowane lokaci ba tare da gajiya ba ko samun watra matsala sai dai ci gaba mai dorewa a kowane hali ga kowa da kowa.
Irin gudunmawar da jami’in ilimi ke badawa wajen samun ingancin abinda zai amfani ganewar abubuwan da ake koyawa daibai da Malamai
Jami’in ilimi yana bada muhimmiyar gudunmawa wajen tsara rayuwar karatu ta ilimin su dalibai wajen ganin ko wane lokaci ana samun ci gaba mai gamsarwa dangane da hazaƙarsu.
Hakkin su ne su tabbatar da makarantu da Malamai suna dai dai da juna su da Malamai manufa anan Malamai suyna koya abinba ya kamata kamar yadda yake cikin manhajar karatu domin samar da ilimi mai nagarta.
Ta yadda za su rika bibiyar yadda ake koyarwa su kasance babu wata amaja, hanyoyi/ dabarun koyarwa, sai yadda dalibai suke fahimtar abinda/ abubuwan da ake koya masu, domin su gano irin wuraren da su Malaman ya dace su kara maida himma domin su dalibai hazakarsu ta karu domin amfanar kansu da kuma al’umma a gaba.
Kai har ma suna wayar da kan al’umma kan muhimman lamurra kamar yadda irin halayyar da su daliban suke da ita, wadda idan aka barai abin ya ci gaba da tafiya a gaba akwai babbar matsalar da a tunkara, saboda irin hakan yana iya shafar lamarin karatun su daliban, abin kuma na iya shafar hazakarsu.
Daga karshe jami’an ilimi wasu muhimman mutane, jami’ai ne da bai kamata ayi masu rikon sakainar ka shi ba, domin suna da babban muhimmanci ga dalibai, Iyaye, da kuma Malamai gaba daya.
Irin gudunmawa da lamarin fasaha yake ga ayyukan jami’in ilimi
Lamarin bangaren fasaha yana bada muhimmiyar gudunmawar tafiyar da aikin sa saboda ta kan ba shi dama ta yin bincike, ya kuma duba da kuma/Nazari kan abinda ya samu domin ya samar da dabaraun koyarwa.Bugu da kari kuma hakan na ba shi dama yadda zai byi mu;amala da mutane kamar su Malamai, shugabannin fannin mulki, da kuma sauarn,
Malamai ko da iya kasance yana amafani ne da fashar sadarwa ta zamani wajen irin hanyoyin da zai bi ko dabaru wajen koyarwa, ya ce fasaha tana taimaka ma say a kasance koda wane lokaci ya ma yana cikin shirin abinda ka iya tasowa, fasaha k9o lamarin ta yana matukar taimakawa, domin samun hanyar da zai amfani da ita wajen gane irin tafarkin ilimin da zai yi amfani da shi domin tabbatar cewa daga karshe ‘yan makaranta ko dalibai za su samun .
Yadda jami’in ilimi yake mu’amala da sauran kwararru a bangaren ilimi
Jami’in ilimi shi en mutumin da ya kamata ya tabbatar da cewa duk wasu manufofi ko tsare- tsaren ilimi yana bi da amfani da su kamar yadda ya dace, duk kuma matakin da ake bukatar ilimi ya zama ya kasance.
Ta hanyar hada kai da wasu kwararru ta bangaren ilimi jami’in ilimi ana bukatar yin hakan domin shi jami’in ilimi ya san yadda zai tafiyar da aikinsa kamar yadda ake tsammanin hakan daga gare sa.Wannan ya hada da yi aiki da Malaman makaranta, shugabannin makaranta, mambobin tafiyar ko gudanar da makarantun,da sauran jami’an ilimi domoin a samar da kuma gudanar da sabbin tsare- tsare ko manufofin ilimi da hanya mafi dacewa da za a tafiyar ko gudanar da su.Dole ne jami’in ilimi ya rika yin lamurransa babu rufa- rufa tare da masu fada aji ya zama lalle ana ci gaba da aiwatar yin abubuwa domin amfanin kowa, wato duk masu ruwa da zaki da suka hada da dalibai da Malamai,da kuma al’umma gaba daya.
Daga karshe shi jami’in ilimi ana sa ran za iyi amfani da duk dabarun da suka kamata domin tabbatar da ana samun nasara yadda dalibai zai kai ga cimma burin mizanin da ake son ya cimmawa da kuma ci gaban lamauran ilimi baki daya.