Rundunar ‘yansandan Jihar Ebonyi, ta sanar da cewa babu wani dansanda da ya rasa ransa a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai ranar Alhamis a Nkomoro, cikin Ebonyi.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Chris Anyanwu a wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da cewa, an kai harin ne kan tawagar ‘yansandan da ke sintiri.
- Manoma Sun Rungumi Shuka Farin Wake Da Auduga Ta Fasahar Zamani
- Xi Ya Halarcin Majalisar Shugabannin Kasashen SCO Karo Na 22 Tare Da Gabatar Da Muhimmin Jawabi
Ya bayyana cewa sabanin yadda aka wallafa a shafukan Intanet, ba a samu asarar rai ba a harin.
Anyanwu ya kara da cewa jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka a harin suna karbar magani a asibiti.
“A ranar Alhamis, tawagar ‘yansandan da ke sintiri a hedikwatar shiyya ta Ezza ta Arewa, sun yi wa tawagar ‘yan bindiga kwanton bauna, inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi.
“Sakamakon martanin da jami’an sintiri suka yi da sauri ya sa ‘yan bindigar suka tsere da raunukan harsasai.
“Bayan wannan arangamar ya bar wata motar sintiri da barayin suka kone amma ba a yi rasa rai a bangaren ‘yansandan ba.
“’Yan sanda biyu da suka samu raunuka sakamakon harin suna karbar magani a asibiti.
“Ya dace a bayyana cewa wannan ita ce sanarwa ta farko kuma tilo da ta fito daga rundunar ‘yansandan Ebonyi kan wannan mummunan harin.
“Mu, a yanzu muna karyata ikirarin cewa an kashe ‘yansanda biyu. Har ila yau, mun tabbatar wa Mista Oko Nweke na HURIDE da wani rahoto irin wannan na karya ba.
“Bugu da kari, babu wani makamanmu da ‘yan bindigar suka tafi da su,” in ji Anyanwu.
Ya kara da cewa, rundunar ‘yansandan ta kama wasu da ake zargi a yankin kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.