Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), ta ce ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar kan karin farashin man fetur da sauran batutuwa, inda ta bayyana rahotannin da ke yawo a matsayin kanzon kurege.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Talata, kungiyar ta ce duk da cewa ta gudanar da taro da gwamnatin tarayya, za a gudanar da gagarumin gangami kamar yadda aka tsara tun farko.
- Chelsea Ta Dauki Lesley Ugochukwu Daga Rennes
- Xi Ya Ba Da Umarnin Ceto Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Da Bala’o’in Yanayi Suka Rutsa Da Su
“Muna so mu sanar da daukacin ‘yan Nijeriya cewa mun kammala wata ganawa da gwamnatin tarayya, inda muka nemi ganin sun saurari bukatun jama’a da ma’aikatan Nijeriya,” in ji shugaban NLC Joe Ajaero.
“Sakamakon wannan taro da aka yi a safiyar yau, duk da haka bai canza komai ba ko kuma tsarin da muka shirya wa kanmu gobe a matsayin masu kula da muradun ma’aikata da jama’ar Nijeriya.
“An shawarci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da duk labaran da ke yawo su yi aiki tukuru. Muna kira ga kowa da kowa da ya taru a jihohinmu da kuma duk inda muke a fadin kasar nan don ba da gudumawar wannan kuduri na bai daya.”
Kungiyar ta bukaci a cire abin da ta bayyana a matsayin “manufofin yaki da talauci” da suka hada da karin farashin man fetur, kudin makaranta, da dai sauransu.