Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce, Allah ne kadai zai hana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu lashe zaben shugaban kasa da za a gudanar a wata mai kamawa.
Gwamnan ya ce “Na yi amanna Allah ba zai hana wannan nagartaccen mutumin cimma burinsa ba. Asiwaju Tinubu mutum ne na kwarai wanda ya yi tasiri sosai ga rayukan mutane da daman gaske.”
- Kungiyar Dalibai Za Ta Shiga Zanga-Zanga Kan Kara Kudin Makaranta A Nijeriya
- Gidauniyar Abdulsamad Ta Bai Wa Hukumar NIS Kyautar 500m Don Inganta Tsaro
Gwamnan ya kara da cewar “Ina da cikakken kwarin guiwar Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa.”
Gwamnan yana wannan bayanin ne a Ilorin, babbar birnin jihar, a wajen taron addu’o’i na musamman da Kungiyar Magoya Bayan Tinubu da Shettima a Arewa ta Tsakiya, ta shirya kan neman nasarar dan takarar a zaben 2023.
Da ya ke samun wakilcin mataimakinsa, Kayode Alabi, gwamna AbdulRazaq ya kara da cewa, “Tinubu mutum ne na kwarai. Shi din nagartaccen mutum ne.”
“Zan sake nanatawa babu wani abin da zai hana Asiwaju cin zaben shugaban kasa baya ga Allah. Na san irin wadannan mutunen kwarai din, Allah ba ya hana musu dama. Babu wani mutum da ya cika dari bisa dari. Allah ne kawai cikakken da ba ya kuskure.”
“Da zarar ya ci zabe, mu kuma za mu ci zabukan 11 ga watan Maris na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi.
“Ina rokon masu zabe da su zabi Tinubu, su zabi APC daga kasa har sama.”
Shi ma da ke jawabi, Shugaban kungiyar, Sanata Dayo Adeyeye, ya ce Nijeriya na bukatar agajin Tinubu cikin gaggawa.
Ya ce, tabbas Tinubu zai iya shawo kan matsalolin da suke addabar kasar nan da suka shafi na tsaro da tattalin arziki.
Shi kuma jagoran shirya taron, Hon. Oyetunde Ojo, cewa ya yi, “Shafaffu da mai masu juya masu mulki ba za su samu gurbi a gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed ba.”
Ya kara da cewa Tinubu zai gudanar da gwamnati ne mai cike da hangen nesa da bin komai bisa tsari domin sabunta kasar nan.