A kwanakin nan, juyin mulkin da ya abku a kasar Niger ya girgiza mutanen duniya. Sai dai wani abun da ya fi ba mutane mamaki, shi ne an ce abkuwar lamarin na da alaka da tallafin da kasar Amurka ta ba kasashen yammacin Afirka ta fuskar aikin tsaro.
Wani shafin yanar gizo na kasar Amurka mai suna “The Intercept” ya ba da labarin cewa, birgadiya janar Moussa Barmou, kwamandan rundunar sojojin kundumbala ta kasar Niger, wanda ke da hannu cikin juyin mulkin din da ya abku a kasar a wannan karo, ya taba samun horo a cibiyar horar da sojoji ta Fort Benning ta kasar Amurka da jami’ar koyon ilimin aikin tsaro ta kasar, kuma yana da alakar kut-da-kut da bangaren sojojin kasar Amurka.
A cewar shafin yanar gizo na “The Intercept”, a shekarun nan, yawan abkuwar hare-haren ta’addanci a yankin yammacin Afirka ya sa kasar Amurka ta samar da karin tallafin aikin soja da ta ga ya dace ga kasashen dake yankin, sai dai batun nan na haddasa matsaloli: Tun daga shekarar 2008, hafsoshin da suka taba samun horon da bangaren Amurka ya bayar sun shiga juyin mulki guda 11 da suka taba abkuwa a yankin yammacin Afirka. Kana a kasashen Burkina Faso da Mali, dake makwabtaka da kasar Niger, hafsoshin da kasar Amurka ta horar da su sun kaddamar da juyin mulki a kalla sau 6, tun daga shekarar 2012.
A ganin Stephanie Savell, daya daga cikin darektoci masu kula da aikin nazarin kudin da aka kashe da hasarar da aka samu wajen yaki na jami’ar Brown ta kasar Amurka, kana kwararriya mai nazarin matakan aikin soja da kasar Amurka ta dauka a yammacin Afirka, babban dalilin da ya haddasa matsaloli a kasar Niger da yankin Sahel gaba daya bai shafi aikin soja ba, saboda haka yadda gwamnatin kasar Amurka take dora muhimmanci kan samar da makamai ga yankin da horar da sojojin kasashen yankin ba zai taimakawa daidaita matsalar da ake fuskanta ba. A cewarta, “Wani mummunan sakamakon da matakin ya haifar shi ne, raunana karfin shawo kan yanayi na sauran hukumomin gwamnatocin yankin, da karfafa karfin rundunar sojoji a kai a kai. Wannan wani dalili ne da ya sa ake samun dimbin juyin mulki a kasashen Niger, da Burkina Faso, da sauran kasashe daban daban.”
Hakika kasar Amurka ta samar da wannan nau’in tallafin aikin soja ne bisa ra’ayinta kan aikin tsaro. A ganin kasar Amurka, muddin dai akwai cikakken karfin soja, to, za a samu cikakken tsaro. Wannan ra’ayi ya sa kasar ta kashe dimbin kudi wajen raya bangaren soja, har ma yawansa ya kai kashi 39% na kudin da daukacin kasashen duniya suka kashe a shekarar 2022 don raya aikin soja, da sanya kasar kafa cibiyoyin soja kimanin 750 a kasashe da yankuna fiye da 100, da girke sojojinta kimanin dubu 173 a cikin cibiyoyin. Amma ko da yake kasar Amurka ta samu cikakken karfin soja, abun nan bai kawo mata cikakken tsaro ba. Maimakon haka, ya haddasa rushewar manyan gine-gine na World Trade Center a yayin harin da aka kai birnin New York a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001, da yadda kasar Amurka ta kaddamar da yaki kai tsaye ko kuma a kaikaice, a kasashen Iraki, da Afghanistan, da Libya, da Ukraine, da dai sauransu, inda ta salwantar da rayukan sojojinta, da kudin jama’arta, gami da haifar ma sauran kasashe da babban rashi da dimbin wahalhalu.
Ganin haka ya sa kasar Sin ta gabatar da shawarar kare tsaro a duk duniya, inda ta yi kira da a daidaita rikici ta hanyar yin musayar ra’ayi da shawarwari cikin lumana. Kana kasar ta yi kira da a dukufa a fannin raya tattalin arziki, don daidaita matsalar samun rikici da rashin tsaro daga tushe, da tabbatar da samun yanayin tsaro mai dorewa. Saboda a ganin Sinawa, nuna fin karfi zai haddasa kiyayya da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa. Dole ne a yi kokarin kare kai bisa adalci, da sauran tunani masu dacewa, sannan za a iya samun ingantaccen tsaro mai dorewa.
Wani abu mai faranta rai shi ne, yawancin kasashen duniya, ciki har da kasashen Afirka, sun yarda da shawarar kasar Sin, ganin yadda suke da ra’ayin tsaro iri daya da na kasar Sin. Bayan abkuwar yaki tsakanin kasar Rasha da ta Ukraine, kasashen Afirka da kasar Sin sun yi kokarin sulhuntawa don neman ganin Rasha da Ukraine sun tsagaita bude wuta da komawa teburin shawarwari. Haka kuma, bayan an yi juyin mulki a kasar Niger a wannan karo, nan take kasar Sin ta yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki na kasar Niger da su lura da moriyar kasar da ta al’ummarta, da daidaita rikici ta hanyar shawarwari. Kana a nata bangare, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta tura shugaban kasar Benin, Patrice Talon, zuwa kasar Niger, don taimakawa daidaita yanayin da ake ciki a kasar.
Dole ne a zauna gaban teburi, domin a fara tattaunawa da shawarwari don neman daidaita rikici. Muna fatan ta wannan hanya za a iya daidaita rikicin siyasa da ya abku a kasar Niger cikin ruwan sanyi, kuma cikin sauri ba tare da wani jinkiri ba. (Bello Wang)