Hukumar zaɓe ta Kasa (INEC) na tunanin amfani da takardun zaɓe na kwamfuta ga waɗanda ba su da katin zaɓe na dindindin (PVC) a lokacin zabe.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana wannan ra’ayi a yayin taron musayar shawara da ra’ayoyi da shugabanni masu gudanar da zaɓe na jihohi (RECs) a Abuja, inda ya ce PVCs ba zai zama ƙa’ida ta kaɗa ƙuri’a ba a yanzu, musamman da shigar da tsarin na’ura zamani (BVAS).
- INEC Ta Bukaci Jam’iyyu Da ‘Yan Takara Su Wanzar Da Zaman Lafiya Kan Zaben Gwamnan Ondo
- INEC Ta Caccaki Gwamnonin PDP Kan Zargin Tafka Magudi A Zaben Edo
Yakubu ya bayyana cewa hukumar ta fitar da rahoton cikakken bincike na zaɓen 2023, wanda ya ƙunshi shawarwari daga jami’an hukumar da masu ruwa da tsaki. Ya kuma jaddada cewa a cikin shawarwarin guda 142 da aka gabatar, 86 na buƙatar matakai na cikin gida, yayin da wasu 48 ke bukatar haɗin kai daga hukumomi kamar jami’an tsaro, masana’antu, da ƙungiyoyin farar hula.
Shawarwarin sun haɗa da kuma bada damar yin zaɓe na farko ga ƴan jarida da sauran ma’aikatan zabe da suke aiki wajen gudanar da zaɓe, wanda zai taimaka wajen tabbatar da cewa duk wanda ke da muhimman ayyuka a lokacin zabe ya samu damar yin zaɓe.
Hakanan, INEC ta kuma bayar da shawarar yin zaɓe daga ƙasashen waje da kuma ƙirƙirar kotun laifukan zaɓe da hukuma ta daban domin sarrafa rajistar jam’iyyun siyasa.