Amina Shehu Lulu ko kuma sabuwar Zeezee kamar yadda wasu ke kiranta ta yi karin haske a kan abin da ya sa ta ke harkar fim, ta kuma bayyana ra’ayinta dangane da abinda wasu ke daukar jaruman masana’antar Kannywood, da kuma burikanta a wannan masana’anta.
Lulu a wata hira da ta yi da DW Hausa ta bayyana cewar asalinta ‘yar birnin Zariya ta Jihar Kaduna ce, amma karatu ya sa ta tafi har Jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin Nijeriya, dangane da dalilin shigarta masana’antar Kannywood Lulu ta ce ba komai ya shigo da ita masana’antar ba illa kasuwanci.
- Hasashen Samun Ruwan Sama A 2025: Shawarwarin Da Kwararru Suka Bai Wa Manoma
- Kasar Sin Na Adawa Da Zarge-Zargen G7 Don Gane Da Tekun Kudancin Kasar
Ni ba ina yin fim ba ne saboda in tarbiyantar ko bata tarbiyar wani ba, illa kawai abinda na sani shi ne ina wannan aiki ne saboda in samu abinda na rufa wa kaina asiri, bayan harkar fim akwai sana’oi da nike yi domin neman kudi, ni yar kasuwa ce ba malamar koyar da tarbiyya ba in ji ta.
Lulu ta kara da cewar duk da cewar babu wata nadama da take yi dangane da kasancewarta jarumar fim amma mutane su sani babu wanda ta sa dole ya kwaikwayi irin rayuwarta ko wani abu da take yi na kashin kai domin kuwa ita ba (Role Model) ba ce in ji ta.
Ni mutum ce kamar kowa dole ne ina yin kuskure kuma ina yin daidai don haka ban tilasta ma kowa ya yi abinda na yi ba, ba lallai ba ne duk abinda na yi ya kasance ya burge kowa don haka idan ka kwaikwayi wani abu daga gareni kai ne ka ji zaka iya, ba zan yi wani abu don gyara ko bata tarbiyar wani ko wata a rayuwa ba.
Da ta ke amsa tambaya a kan rayuwa kafin samun daukaka da kuma bayan samun daukaka, Lulu ta amsa da cewar akwai banbanci sosai a rayuwata ta baya da kuma yanzu, saboda yanzu mutane da dama sun sanni ba kamar kafin in fara harkar fim ba, a wancan lokacin mutane basu damu da kai ba amma yanzu kuma ka samu masoya da wadanda ke ganin ba daidai kake yin abubuwa ba, saboda haka dole ne abubuwa su canza sosai.
Daga karshe jarumar ta ce ba ta fatan ace ta shafe shekaru fiye da goma a masana’antar ta nishadi, don kuwa ba ta son ace sai ta tsufa sannan za ta daina harkar fim, ina fatan ganin nan da shekara goma ace na koma gefe na baiwa matasa masu tasowa wuri domin kuwa bani son ace sai na tsufa a masana’antar kafin a daina dora mani na’urar daukar hoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp