Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su — ɗaya na sanye da dogon riga ruwan ƙasa mai duhu, dayan kuma cikin launin kore. A cikin bidiyon, an gansu suna amsa tambayoyin da ɓarayin daji ke musu a cikin harshen Hausa.
A bidiyo na farko mai tsawon daƙiƙu 26, ɓarayin sun tambayi mutanen da aka sace daga ina aka kama su. Sun ce daga Kucheri. Suka ce sun je Funtua. Lokacin da aka tambaye su dalilin zuwa Funtua, sun ce sun je kamfaninsu.
- Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Mayaƙan Bello Turji Da Yawa A Zamfara
A bidiyo na biyu mai daƙiƙu 30, ɓarayin sun tambayi mutumin da ke cikin dogon riga ruwan ƙasa dangantakarsa da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal. Ya ce, “Ni ɗan uwansa ne.” Ɓarayin suka sake tambaya ko suna da uba da uwa ɗaya, sai ya amsa da eh. Daga nan sai suka tilasta masa ya sake maimaitawa da ƙarfi cewa shi ɗan uwan Gwamna Dauda Lawal ne, wanda ya yi.
Ɓarayin suka ƙara da cewa: “Idan ba a biya kuɗin fansa ba, za mu kashe ku. Ku kira Dauda ya shirya mana kuɗin.”
BINCIKENMU:
Rahoton LEADERSHIP ya tabbatar da cewa wannan ikirari ƙarya ne. Bincike ya nuna cewa ba wanda aka sace daga cikin mutanen da ke bidiyon yana da alaƙa da Gwamna Dauda Lawal. Haka kuma, binciken ya nuna cewa ƴar uwar Gwamnan da aka sani mace ce, ba namiji ba.
Hakanan, mutumin da ke cikin bidiyon na bayyana cikin tsananin firgici da damuwa, alamar cewa yana fuskantar tilas daga barayin daji da suka umurce shi da ya faɗi abin da suke so.
Da yake martani kan bidiyon, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa wannan wata sabuwar dabara ce da ɓarayin suka bullo da ita don jawo hankali. Ya ce, “Idan aka kalli bidiyon da kyau, za a ga irin damuwar da waɗanda aka sace suke ciki. Wannan sabuwar hanya ce da ɓarayin daji ke amfani da ita.”
Ya ƙara da cewa, gwamnati tana ɗaukar matakai domin ceto waɗanda aka sace tare da mayar da su cikin aminci ga iyalansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp