Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Barkan ku da wannan lokaci, cikin filinmu na MARURUN ZUCIYA, fili na musamman wanda muke tattaunawa a kan abubuwan da suke ci wa al’umma tuwo a kwarya, kamar kowane mako yau ma filin na tafe da wani batun da za mu yi magana a kai.
A wannan karan zan yi magana ne a kan barace-barace, alal hakika kowa ya riga ya sani babu kyau, kuma a yadda masana masu ilimi suke fada cewar; yawan barace-barace yana kawo talauci.
Wanda a arewacin Najeriya abun ya zo da sabon salo ta hanyar yin bara ta ko’ina, ba namiji ba mace, ba babba ba yaro, ba tsoho ba tsohuwa, ba budurwa ba saurayi, bara ta zo da abubuwa kala daban-daban, wasu ma ba za su kwatantu ba. Shin ta ina za mu magance wannan matsalar?
Kira na ga dukkanin wanda ya ke da, ikon fada a ji ko gyarawa a arewacinmu daya kalli al’amarin da idon basira, domin gaba abun ba zai haifar da da mai ido ba. Shin ta ya za mu magance wannan matsalar?
Abun dubawa da nazari shi ne; idan za ka taimaki dan wani to, ka sani danka ka taimaka. Domin idan kana magidanci kana ganin ‘ya’yanka kawai ka ke taimakawa to, wadanda baka taimakawa ba su ne fa abokan ‘ya’yanka, idan wadannan yaran baka yi kokarin hanasu bara ba to, wataran kai ma za ka iya mutuwa ba tare da ka samu me taimakawa danka ba, haka rayuwa take, amma idan ka gina wani to, shi ma zai zo ya taimaki danka.
Ni ina ganin ta hanyoyin da za a magance bara banda gwamnati, ba iya gwamnati ce kadai za ta magance yawan barace-baracen nan ba, mu kalli al’amarin, idan yunwa ce da fatara da halin da a ke ciki na wannan yanayi shi ne; Idan marayu ne mu dauki gabar taimakawa marayu ta gidaje, idan abinci ne mu taimaka musu da abinci, idan kuma babu marayun to, mu kalli almajirai koda mutum daya ne mu dauki kwano ya rika bawa kowanne almajiri, domin abun yayi yawa.
Mu kalli hanyoyi da gabobi ta yadda za mu magance wannan matsalolin gaskiya abun kunya ne, gaba abun ba zai haifar mana da abu mai kyau ba, saboda kullum abun sake gaba ya ke yi, kara rubanya ya ke, manyanmu da shuwagabanninmu su kuma sun ki kallon abun a matsayin wani al’amari ne da zai iya shafar arewa kuma ya ba mu matsala nan gaba.
Idan ka yi taimako kanka da ‘ya’yanka ka taimaka, Allah ya tsare mu ya kare mu, Allah ya kawo mana mafita cikin wannan al’amarin.