Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya nisanta kansa daga wata kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar, inda ya bayyana cewa ba shi da masaniya a kan yarjejeniyar.
Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Baba Halilu Dantiye, da sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, suka fitar, Gwamnan ya bayyana cewa bai da masaniya kan kwangilar ko tsarin da aka bayar da ita.
- Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato
- Mutum 68 Sun Mutu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Sudan
Gwamna Yusuf, ya umurci Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) da ya fara gudanar da bincike cikin gaggawa dangane da zarge-zargen.
Ya kuma buƙaci al’ummar Kano da su ci gaba da haƙuri a yayin gudanar da binciken, yana mai ba su tabbacin cewa za a gudanar da binciken cikin gaskiya don bankaɗo lamarin.