Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ajibola Bashiru ya bayyana cewa babu wani shiri na bayar da Nijeriya karkashin tsarin jam’iyya daya, amma jam’iyyar za ta ci gaba da lashe zabe a kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa dimbin magoya bayan jam’iyyar jawabi a sakateriyar jam’iyyar da ke Abuja, wanda suka magoya bayan jam’iyyar suka mamaye shalkwatan domin nuna goyon baya ga shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.
- Umarnin Kotu Da Ya Tabbatar Da Dakatar Da Ganduje Bai Inganta Ba, Ba Za Mu Yi Biyayya Ba – APC
- Garkuwa Da ‘Yan Makaranta: Nijeriya Ba Za Ta Sake Biyan Kuɗin Fansa Ba – Tinubu
Ya ce, “Mu ba mu ce dole sai Nijeriya ta koma tsarin jam’iya daya ba. Amma mun gina jam’iyyar da za ta dunga lashe zabe a ko da yaushe. Muna tabbatar da cewa akwai kudin samar da ilimi da kuma sauran ababen more rayuwa.
“Makiya ba su isa su hana mu ci gaba ba. Muna bayar da goyon baya ga jagoranmu, mai girma Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa yadda yake aiwatar da shirinsa na sake farfado da kasar nan. Muna kara hada kai karkashin jagorancin shugaban jam’iyyarmu na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.”
A kwanan nan dai Ganduje yana fuskantar ce-ce-ku-ce game da dakatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC.
Amma da yake jawabi ga dimbin magoya bayan jam’iyyar, Ganduje ya ce wasu ne kawai suke jin tsoron yadda yake aiwatar da lamuran jam’iyyar, wanda suka kulla masa kutun-gwila.
“Sun jin tsoron yadda muke sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar. Suna jin tsoro ne saboda muna samun mutane wadanda suke yin tururuwa wajen shiga jam’iyyar a ko’ina a fadin kasar nan. Wannan shi ya haddasa musu tsoro a zukatansu.
“Suna sa ido a 2027, amma a wannan lokaci babu wani gurbi. Shugaban kasarmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ne zai ci gaba da mulkin Nijeriya idan Allah ya yarda.”
Da yake kira ga magoya bayan APC su yi watsi da abun da ya kira dirama, Ganduje ya ce, “Mun fahimci abubuwan da suke yi. Wasan kwaikwayon siyasa ne. Suna yin wannan dirama ne domin su boye gazawarsu. Ba za mu taba barin su ci gaba da wannan ba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp