Sakamakon rahotannin da ke yawo na yunkurin wasu gwamnonin arewa na shirin yin sulhu da ‘yan ta’addan daji, tsohon shugaban kungiyar Miyetti Allah Cat-tle Breeders na kasa, Alhaji Hussaini Yusuf ya ce sulhu alheri ne, domin manzon Allah ya tabbatar da hakan.
Ya kara da cewa ba su hana a yi sulhu da ‘yan ta’adda ba, amma a bar jami’an tsa-ro su yi aikinsu.
- Zamfara: Shugabanninmu, Ku Yi Hankali Da ‘Yan Kanzagi
- An Kaddamar Da Shirin Baje Kolin Inganta Harkar Noma Da Sana’o’i A Kano
Tsohon shugaban ya ci gaba da cewa maganar sulhu da ‘yan ta’adda masu dauke da makamai a baya gwamnatin Zamfara da wasu gwamnoni sun yi irin wannan sulhun amma abin bai haifar da da mai ido.
Ya ce babu tabbas idan an yi sulhun ‘yan ta’addan za su ajiye makamansu, to ma ta ya ya za a yi sulhu wanda aka ka wa laifi ne ke neman sulhu ba mai laifin ba.
A cewarsa, idan da gaske su ‘yan ta’addan sun amince da cewa sun yi laifi, su ne ya kamata su nemi yin sulhu ba gwamnati ba, idan ma ya zama gwamnatin ta matsa kan maganar sulhu, suna fatar Allah ya sa a yi da kyakkyawar niyya kuma a bar jami’an tsaro su ci gaba da aikinsu.
“Barayin nan na san ba za su ajiye makamansu ba, domin an yi a baya kuma abin bai yi wani tasiri ba, da suka dauki makami ba za su iya fada maka laifin da aka yi musu da ya sa suke fada wa talakawa suna kwashe su da lalata abinci da duki-yoyinsu, idan da gaske ne, to su manyansu su fito gwamnati ta ware wuri ‘yan ta’addar nan su kawo makamansu a hannun gwamnati.
“Babban matsalar nan, akwai wadanda ke daukar makamai a matsayin ‘yan banga kuma su ba ‘yan sa kai ba ne. Ka ga maganar ‘yan banga da ke aiki da jami’an tsa-ro ban goyon bayan shi ba, domin suna da kwarewa saboda gogayyarsu da ja-mi’an tsaro, amma wasu da amfani da wannan dama su na farmakan jama’a,” in ji shi.