ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zamfara: Shugabanninmu, Ku Yi Hankali Da ‘Yan Kanzagi

by Imam Murtadha Muhammad Gusau
3 years ago
Zamfara

Da farko zan fara da gaisuwa kamar yadda muka saba, Assalamu alaikum wa rahmatullahi Ta’ala wa barakatuhu.  Ya ‘yan’uwana al’ummar Jihar Zamfara masu albarka (Zamfarawa), ya kamata mu san cewa, da Dauda Lawal da ya zama Gwamnan Jihar Zamfara da kuma Bello Muhammad Matawalle da ya zama Ministan Nijeriya, duk wannan daga Allah ne, a cikin su babu wanda ya ba wa kansa wannan matsayi.

Sannan a cikin nasu babu wanda wayonsa ko dabararsa ta ba shi wannan matsayi. Mun yi imani da Allah a matsayinmu na musulmi cewa, shi kadai ne ke bayar da mulki da matsayi ga wanda ya so. Don haka, ya zama wajibi mu yi musu addu’a tare da fatan alhairi, Allah ya ba su sa’a da nasara, ya kuma sa a ce gwamma da aka yi. Allah kuma ya sa su zamar wa Jihar Zamfara alhairi da ma Nijeriya baki daya tare da fitar da su kunya, duniya da ta lahira, amin.

  • Sin Ta Fara Shirin Aikewa Da Sinawa Zuwa Duniyar Wata Nan Zuwa 2030
  • Rage Radadin Cire Tallafi: Gwamnati Ta Baiwa  Kowacce Jiha Naira Biliyan Biyu A Kashin Farko

Amma mutum ya koma gefe yana soke-soke da zage-zage da cin mutunci; ko ya kasance yana rubuce-rubucen banza a kafafen sada zumunta, ko shiga rediyo ko talabijin yana babatun banza, don goyon bayan Gwamna ko Minista, to wallahi duk wannan babu inda zai kai mu, domin kuwa bai dace ba. Sannan a matsayinmu na musulmai, mu sani wannan haramun ne kai tsaye, haramun ne, haramun ne!

ADVERTISEMENT

Duk mai kishin Jihar Zamfara da Nijeriya da gaske tare da son a samar da tsaro da ci gaba da kwanciyar hankali, to kamata ya yi ya dage da addu’a da rokon Allah (SWT), ya sa wadannan shugabanni su zama alhairi a gare mu baki-daya.

Don haka, ina sake yin kira ga Zamfarawa da mu ji tsoron Allah, mu yi musu addu’a, mu kuma yi wa jiharmu da kasabaki-daya addu’a.

LABARAI MASU NASABA

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

Haka zalika, duk siyasar da muke yi, mu rika tunawa cewa mu musulmi ne. Sannan shi musulmi, yana da dokoki da ka’idojin da suke yi masa jagoranci a cikin dukkanin rayuwarsa, ba haka kawai yake rayuwa sagaga ba. A tare da shi akwai Mala’iku masu rubuta dukkannin abin da ya aikata na alhairi ko sharri.

Sannan, su kuma wadannan shugabanni guda biyu, wato Gwamna Dauda Lawal da kuma Minista Muhammad Bello Matawalle, ina rokon su tare da yin kira da su ji tsoron Allah (SWT). Su kuma sani cewa, su jarabawa ce da Allah ya jarrabi Zamfarawa da su. Don haka, ya zama wajibi su hada kai domin kawo wa Jihar Zamfara da Nijeriya baki- daya alhairi da ci gaban da zai amfani kowa da kowa.

Har wa yau, ka da su yarda da masu zuga da ‘yan bani-na-iya, ‘yan kanzagi da banbadanci, wadanda su a koda-yaushe, fadan shugabanni da rigingimunsu sh ine hanyar cin abincinsu. Irin wadannan mutane wallahi babu wani alhairi a tare da su kwata-kwata illa sharri.

Gwamna Dauda Lawal da Minista Muhammad Bello Matawalle, ku sani cewa a matsayinku na jagororin Zamfarawa, Allah zai tashe ku a gabansa a filin alkiyama, domin yi muku hisabi a kan wannan jagoranci da ya dora muku. A wannan rana wallahi babu wani magoyin bayanku da zai iya fitar da ku, face ayukkanku na alhairi da kuka yi. Don haka, ka da ku taba yarda da zugar wani magoyin baya, wanda a wannan rana ta lahira shi ma ta kansa yake yi, kuma kuma kuna taku ta kan.

Wallahi kaunar da nake yi muku tsakanina da Allah da kuma kishina ga jihata da kuma kasa baki-daya ne yasa na yi wannan rubutu. Domin kuwa, ina kallon duk abin da ke faruwa a fadin wannan jiha tamu, wanda idan wannan lamari ya ci gaba a haka, ko shakka babu jiharmu da al’ummarmu ba za su ji dadi ba.

Ku manta da maganar banbancin jam’iyyar da ke tsakaninku, ku manta da banbancin siyasar da ke tsakaninku, ku ji tsoron mahaliccinku, ku kalli al’ummarku, ku yi kokari ku hada kai, domin tunkarar rashin tsaro da yunwa da talaucin da ke addabar Jiharmu ta Zamfara mai albarka.

Muhammad Bello Matawalle, a matsayin da Allah ya ba ka na Ministan Tsaro, ya zama tilas in dai har dai kana son tsira a gaban Allah, ka hada kai da Gwamna Dauda Lawal, ku yi aiki tare, domin samar da kyakkyawar natija.

Haka nan, Gwamna Dauda Lawal, a matsayinka na Gwamnan Jihar Zamfara, wanda Allah ya damka wa amanar tsaron Jihar Zamfara da ci gabanta, da zaman lafiyarta a hannunka, kai ma ya zama tilas in dai kana son tsira a gaban Allah, ka hada kai da Minista Muhammad Bello Matawalle, ku yi aiki tare ba tare hangen wani banbaci na jam’iyya ko siyasa ba, domin kawo wa jihar da ma Najeriya baki-daya ci gaba.

Wannan ita ce gaskiyar magana, wadda duk wani masoyinku na gaskiya zai fada muku. Duk wanda zai gaya muku akasin haka kuma, mikiyunku ne. Mikiyinku wanda yake so ya jefa ku cikin rami, ya bar ku da jangwam a gaban Allah (SWT).

Bugu da kari, dukkanin manyan ‘yan siyasarmu na Jihar Zamfara, su ma ya zamar musu wajibi su mayar da hankali wurin zamar wa jihar da kasa baki-daya alhairi. Musamman kamar Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura, Tsohon Gwamna Sanata Abdul-Aziz Yari, Tsohon Sanata Marafa, Dan Majalisa Aminu Sani Jaji, Sanata Ikra Aliyu Bilbis, Sanata Sahabi Ya’u Kaura, Dan Majalisa Kabiru Amadu Mai Palace da sauran makamantansu, ya zama wajibi a gare mu mu ji tsoron Allah, mu kuma zama alhairi ga jiharmu mai albarka.

Gaskiyar magana ita ce, dukkanin ku kuna da magoya baya da masoya, akwai dimbin jama’ar da suke bayanku, don haka wuka da nama duk a hannunku suke. Idan kun gyara kun sani, idan kuma kuka bata nan ma kun sani.

Sannan duk wanda yayi da kyau, ya sani, Allah zai yaba haka nan kuma al’umma ma za su yaba. Duk kuma wanda ya bata, ya sani cewa zai jawo wa kansa fushin Allah, sannan kuma al’umma za su yi Allah wadai da shi.

Allah ya sa mu dace, ya ganar da mu gaskiya, amin.

 

Zamfara
Imam Murtadha Muhammad Gusau
+ postsBio
  • Imam Murtadha Muhammad Gusau
    https://hausa.leadership.ng/author/imam-murtadha-muhammad-gusau/
    Matsalar Tsaron Nijeriya:  Ku Faɗi Alkairi Ko Ku Yi Shiru!
  • Imam Murtadha Muhammad Gusau
    https://hausa.leadership.ng/author/imam-murtadha-muhammad-gusau/
    Tsakanin Matawalle Da Dauda Lawal…
  • Imam Murtadha Muhammad Gusau
    https://hausa.leadership.ng/author/imam-murtadha-muhammad-gusau/
    Al’ummar Arewa: Bango Ne Ya Tsage Kadangare Ya Samu Wurin Shiga
  • Imam Murtadha Muhammad Gusau
    https://hausa.leadership.ng/author/imam-murtadha-muhammad-gusau/
    Tsarin Mulkin Firayminista: ‘Yan Arewa Mu Yi Taka-tsan-tsan

MASU ALAKA

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki
Bakon Marubuci

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

June 12, 2026
A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara
Bakon Marubuci

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

June 12, 2026
‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa
Bakon Marubuci

‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa

June 5, 2026
Next Post
An Rufe Kasuwar Saye Da Sayarwar ‘Yan Wasan Kwallon Kafa Ta Bana A Turai

An Rufe Kasuwar Saye Da Sayarwar ‘Yan Wasan Kwallon Kafa Ta Bana A Turai

LABARAI MASU NASABA

Yawan Man Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Da Ganga 177,000 A Janairu

Dalilin Da Ya Sa Matatar Dangote Ta Kara Habaka Tura Man Fetur

June 13, 2026
Zan Saki Nnamdi Kanu Idan Na Zama Shugaban Ƙasa – Peter Obi

Zan Saki Nnamdi Kanu Idan Na Zama Shugaban Ƙasa – Peter Obi

June 13, 2026
NPA Ta Tara Kudin Shiga Naira Biliyan 758.2 A 2024

NPA Da Birtaniya Sun Kulla Yarjejeniyar Zamanantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya

June 13, 2026
Sukar Da Ake Yi Wa Mbappé Ta Yi Yawa — Dembélé

Sukar Da Ake Yi Wa Mbappé Ta Yi Yawa — Dembélé

June 13, 2026
Yadda Rufe Kan Iyakoki Ke Ci Gaba Da Zama Barazana Ga Tattalin Arzikin Nijeriya

Yadda Rufe Kan Iyakoki Ke Ci Gaba Da Zama Barazana Ga Tattalin Arzikin Nijeriya

June 13, 2026
Mutum 53,000 Ke Mutuwa Duk Shekara Sakamakon Amfani Da Gurbataccen Abinci —Gwamnati

Mutum 53,000 Ke Mutuwa Duk Shekara Sakamakon Amfani Da Gurbataccen Abinci —Gwamnati

June 13, 2026
Manufar Soke Haraji Ga Kasashen Afirka Ta Sin Ta Samar Da Sabbin Damammaki Ga Nahiyar

Manufar Soke Haraji Ga Kasashen Afirka Ta Sin Ta Samar Da Sabbin Damammaki Ga Nahiyar

June 12, 2026
2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

June 12, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?

Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?

June 12, 2026
Zhang Guoqing Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Koli Na “Hadin Kai Don Bunkasa Tattalin Arzikin Duniya”

Zhang Guoqing Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Koli Na “Hadin Kai Don Bunkasa Tattalin Arzikin Duniya”

June 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.