Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta ce ba ta kai mamaya ofishin Babban Bankin Nijeriya ba kamar yadda wasu rahotanni suka nuna.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ya fitar, ya kuma ce rundunar ‘yan sandan sirrin ba ta kama gwamnan CBN, Godwin Emefiele ba.
- Musulman Sun Fusata Da Matakin Gwamnatin Bauchi Kan Makabarta
- DSS Ta Karyata Yin Kawanya A Shalkwar CBN, Bayan Emefiele Ya Dawo Kan Aiki
Da yake karyata rahotannin da kafafen yada labarai suka yada na kama shi, kakakin DSS, ya bayyana hakan a matsayin labaran bogi.
“An jawo hankalin Hukumar Tsaro Farin Kaya (DSS) kan labarin karya da ake yadawa cewa jami’anta sun mamaye Babban Bankin Nijeriya tare da kama gwamnansa, a yau 16/1/23. Wannan labari ne na karya kuma yaudara ce,” in ji sanarwar.
A halin yanzu dai Emefiele ya koma bakin aikinsa bayan hutun da ya yi a kasar waje.
Daraktan Sadarwa na CBN, Osita Nwanisobi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnan babban bankin ya koma aiki tare da sabunta kwarin guiwa don gudanar da aikinsa gabanin taron kwamitin kula da harkokin kudi na farko (MPC) na shekarar nan a ranar 23 zuwa 24 ga watan Janairu, 2023,” in ji sanarwar.
“Emefiele ya ci gaba da jajircewa wajen gudanar da aikin da ke gabansa daidai don tsarin manufofin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
A kwanakin baya ne dai DSS ta sanya wa Emefiele kahon zuka wanda suka kai kara kotu bisa zarginsa sa daukar nauyin ta’addanci.
DSS ta garzaya wata kotun Abuja domin samun sahalewa don ta kamo gwamnan babban bankin bisa zargin daukar nauyin ta’addanci da kuma laifukan da suka shafi tattalin arzikin kasa, amma mai shari’a Maryam Hassan ta babbar kotun, ta yi watsi da bukatar ta DSS.
Bayan haka, alkalin ta DSS kama, gayyata, ko tsare Emefiele, inda ta bayyana zargin ta’addancin da DSS ke yiwa gwamnan CBN a matsayin daukar zargi mara tushe.