Sanata Ali Mohammed Ndume, ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Borno, ya ce ba ya goyon bayan dakatar da zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Ribas, Simi Fubara, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar kamar yadda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Ndume ya bayyana cewa, ko da yake matsalar tsaro tana ƙara taɓarɓarewa a jihar, cire gwamnan ba hanya ce mai kyau ba, kodayake yana goyon bayan kafa dokar ta ɓaci.
- Sin Ta Mika Tallafin Wasu Jirage Marasa Matuka Na Inganta Noma Ga Kasar Zambia
- Gidauniya Ta Jajanta Wa Waɗanda Hatsarin Tankar Gas Ya Shafa A Abuja
Ya ce: “Ta yaya za a cire zaɓaɓɓen gwamna don a maye gurbinsa da soja?”
Sanatan ya kuma mayar da martani kan zargin cewa majalisar dattawa ta gaza sasanta rikicin majalisar dokokin Ribas, wadda ta rabu gida biyu har zuwa lokacin da Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci.
A halin yanzu, sabon Kantoman soji da Shugaba Tinubu ya naɗa, Ibok Ete Ibas, ya fara aiki a jihar, inda ya gana da manyan Kwamandojin tsaro da jami’an gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp