Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Mista Peter Obi ya ce shi fa bai kosa da sai ya zama shugaban kasar Nijeriya ba, amma babbar manufarsa da burinsa shi ne ya yi wa kasa aiki.
Obi wanda ya yi wannan magana a lokacin da yake mayar da martani jim kadan bayan ya amshi lambar yabo na gwarzon dan siyasar LEADERSHIP na shekarar 2023 a taron bayar da kyaututtuka da kamfanin LEADERSHIP ya shirya a Abuja, ranar Talata.
- Rikita-rikitar Sauka Da Komawar Sheikh Daurawa Shugabancin Hisbar Jihar Kano
- Babban Taron LEADERSHIP Ya Zakulo Yadda Za A Ceto Nijeriya
A cewar dan takarar shugaban kasan, abun kunya ne a ce kasar Ukraine da yaki ya daidaitata take bai wa Nijeriya tallafin hatsi, a daidai lokacin da Jihar Neja kadai za ta iya noma abincin da za a ciyar da Afrika gaba daya.
“Ina mika godiya ta ta musamman ga kamfanin buga jaridu na LEADERSHIP bisa shirya wannan muhimmin taro. Mun ji jawabai mabambanta daga bakunan masu gabatar da jawabai.
“A wajen wannan kyauta, abun godiya ne ga madaukakin Sarki. Idan ina da dama zan bayar da wannan kyauta ga dukkanin ‘yan kasata.
“Ni dai ban kosa sai na zama shugaban kasa ba, sai dai na matsu da in yi wa Nijeriya aiki ne kawai,” in ji shi.
Obi ya kara da cewa, ya zama wajibi matasan Nijeriya su kasance masu amfanar da kansu da wani don a magance talauci da ayyukata muggan laifuka.