Sabon marubuci da ma iya cewa ya shigo duniyar rubutu da kafar dama, wato ALKASIM SALIHU wanda aka fi sani da A.S. Aikawa, ya bayyana irin yadda salon rubutunsa yake da ya bambanta da na sauran marubuta, da ma tarihin rubuce-rubucensa a cikin tattaunawarsa da wakilinmu ADAMU YUSUF INDABO. Ga yadda tattaunawar tasu ta Kasance:
Wane ne Alkasim Aikawa?
Da farko dai sunana Alkaseem Abdullahi Salihu Aikawa amma ana kira na da ‘A.A.S AIKAWA.’ Ni haifaffen jihar Kano ne cikin unguwar Aikawa Dala Local Gobernment. Amma yanzu ina unguwar Mandawari opposite police station. Na yi karatun boko tun daga matakin nasery har zuwa matakin N.C.E. Ina da shekara ashirin daidai a duniya. Wannan shi ne takaitaccen tarihina.
To ya aka yi ka samu kan ka a matsayin marubuci?
To gaskiya a farko dai na kasance mai son yawan karance karance irin su jaridu haka, mujallu, da sauran irin littafan ruwan bagaja, shehu umar, magana jari ce. Daga baya na ji ina sha’awar yin rubuce rubuce musamman a bangaren zamantakewar al’umma da kuma abin da yake faruwa yanzu a a duniya, da yadda al’umma suka tabarbare suka kauce daga koyarwa musulunci suka kama al’adun yahudu da nasara. Musamman matasa tunda su ne kashin baya a kowacce al’umma, sannan kuma rubutu yana da tasiri sosai wajan isar da duk wani sako da kake son isarwa, yanzu sai ka ga ka kai sakon ka in da ba ka yi tunanin zai je ba, kuma shi rubutu yana iya shiryarwa ma’ana ya yi gyara, ko kuma ya lalata ma’ana ya bata. Dan haka wannan dalilin ya sa na fara rubutuna na farko a kan rayuwar matasa inda na sa masa suna MAKOMAR MATASA. wannan shi ne a takaitaccen bayanin yadda na tsinci kaina a matsayin marubuci.
Ke nan littafin Makomar Matasa shi ne littafin farko da ka fara rubutawa?
Haka ne shi ne littafina na farko da na fara rubutawa. Wanda babban jigon labarin shi ne rayuwar matasa, da farko na yi la’akari ne da yadda matasa suka zama a wannan zamanin, na dauki kanta ita kalmar matasa din su wane ne matasa, ya za a yi matashi ya amsa sunansa na nagartaccen matashi, da abubuwan dake lalata matasa da kuma hanyoyin kawo gyara na yadda rayuwar matasa zata inganta ta yi kyau har zama abin alfahari. Duba da yadda matasa su ne suke taka muhimiyyar rawa wajan lalacewar al’umma ko kuma gyaruwarta. To zan amfani da wannan damar ma na fadi wane ne matashi. Idan na ce wane ne matashi ina nufin cikakken matashi nagari wanda yake zama shi ne ginshikin samuwar al’umma ta gari, tabbas mafi girman amfani, tasiri, da kuma girma acikin al’umma su ne matasa. Dalilina shi ne ko a kundin kidayar al’umma na duniya {Census} za ka ga matasa su ne mafi yawan rinjaye a duniya baki daya. Sabida haka na zabi na yi Magana ne a kan matashi domin girma da yawan da suke da shi, da kuma farkar da su domin su gane muhimmancinsu da irin rawar da suke takawa a cikin al’umma. Domin har idan muna so mu kawo gyara a cikin al`umma to fa dole sai an waiwayi matasa, an jawo hankalin matasa, an nuna musu hanyar da ta dace domin gudun yin tufka da kuma warwara.
A wani dan bincike da na yi na gano cewa masana ilimin halayyar dan adam sun fadi adadin shekarun da matashi yake farawa, wasu sun ce suna farawa ne daga shekara sha biyar zuwa arba`in, wasu kuma sun ce daga shekara ashirin zuwa arba`in. in ka duba sosai ka lura za ka ga gaba daya a tsakanin shekarun nan ne mutum yake kamala gina jikinsa da kwakwalwarsa . kuma a wannan shekarun ne gabobi suke kara tasawa, tunani yakan yi wa mutum yawa har zuwa lokacin da mutum ya kai shekara ashirin da biyar. Daga nan sai masana suka ce tsawo da girman kasusuwa ya kare, sai dai kuma tsoka ta cigaba da yaduwa ga wanda Allah ya baiwa yanayi na cikin jiki da yakan cigaba da karuwa. Idan muka duba sannu a hankali za mu ga cewa, a wannan shekarun da na ambata a baya tunani kan farawa kamar yadda na fada, bayan tunani sai me, su ne lokacin da mutum yake gina mene ne zai yi a rayuwarsa shi ne lokacin da mutum yake fara tunanin yin karatu ko kuma akasin haka, su ne dai lokacin da mutum kan fara saka burin wani abu a zuciyarsa, zan yi kaza, zan haifar da kaza zan tafi kasuwa, zan tafi neman ilimi, ina son in zama mai kudi ina son in zama malami, ina son in zama dan kasuwa, ina son in zama mai yada addini, a’a duk ba wannan ba ya zan yi in ciyar da al`ummata gaba, ya zan yi in taimaki jama`a, lokaci ne da mutum yake tunanin yin aure domin tara `ya`ya, lokaci ne na tunin (MATA`UL HAYAT) wato kawace-kawacen rayuwa. Wannan a takaice ke nan.
To tun yaushe ka fara rubutu?
Na fara rubutu a shekarar 2022. Kuma yanzu haka na rubuta littafi guda biyar su ne: Makomar Matasa, Rayuwar Mu A Yau, Ina Mafita, Arewa Mu Koma Ga Allah, Kowa Ya Sai Rariya… Amma a cikinsu Makomar Matasa ne kawai aka yi dab’insa, ragowar hudun kuma sai zuwa gaba in Sha Allah.
To ya ka fuskanci rubutun wadannan littafai a matsayinka na sabon marubuci?
Gaskiya rubutu ga sabon marubuci yana da matukar wahala, amma shi komai a rayuwa idan ka sa a ranka za ka iya, to in sha Allah da taimakon Allah za ka ga ka cimma nasara akan abu, muddin ka sanya Allah a cikin lamuranka ka kuma sa a zuciyar ka cewa za kai to zakai din, dan haka da zan fara rubutuna na ji zan iya yi din kamar yadda kowa yake yi kuma na hada da neman taimakon Allah, shi ya sa ban fuskanci wata matsala ba a rubutuna. Illa kawai ince shi harkar rubutun littafi muddin za ka buga shi ya fita a takarda to sai kana da kudi domin abu ne da yake bukatar kudi wajan bugunsa, yanzu kamar ni babban burina shi ne wannan littafin na makomar matasa in samu damar da zan buga shi da yawa, in san samu ne har kaddamar da shi ya kamata na yi domin ya yadu sosai yadda al’umma za su amfana.
Matsayinka na wanda ya fara rubutu da kananun shekaru, to ba ka fuskanci kalubale musamman daga gida ba?
Gaskiya ban fuskanta ba, na samu hadin kai da goyon baya dari bisa dari daga gida, sun samun albarka tare da fatan nasara a kan lamurana, sabida littatafaina ina yin su ne a kan halayyar da zamantakewar dan adam, ba nanaye ko rashin da’a nake rubutawa ba.
Cikin littattafanka guda biyar ko akwai wanda ya walagigi da kai yayin rubuta shi?
Gaskiya littafin da ya ba ni wahala wajan rubutwa shi ne dai littafin makomar matasa, gaskiya na wahala sosai wajan rubuta shi, sabida ni na tafa shi a computer wani lokacin sai na shagala ina typing na manta ban yi sabing ba, sai nepa su dauke wuta sabida computer tawa tana da matsalar batir, dan akwai lokacin da gaba daya computer ta dauke ta ki aiki sai aka yi format nata kuma kaf aikina sai da ya goge, sai da na sake sabon typing shi yasa ma ya dauki lokaci sosai wajan fitowarsa.
To a wanne lokaci da kuma yanayi Malam Alkasim ya fi jin dadin yin rubutu?
Gaskiya na fi son rubutu da daddare musamman irin karfe sha biyu na dare haka sabuda lokaci ne da sawu ya dauke babu hayaniya sannan kuma idia ta fi zuwar min a lokacin. Sannan ni dai na fi jin dadin rubutu a lokacin ina jin yunwa sabuda in na ci na koshi kasala ma lullube ni take, sannan da lokacin walwala nakan ji dadin rubutu a wannan lokacin.
To wanne haske ka soma gani daga fara rubutunka zuwa yau?
Tabbas akwai haske domin dalilin rubutuna na sake samun wata wayewa ta bangaren mu’amala sannan kuma dalilin rubutuna ya sanya manyan mutane da dama sun neme ni kuma sun yaba min a kan kwazona da kuma basirata. Sabuda haka babu abin da zan cewa Allah sai godiya.
To ya maganar kunguyoyin marubuta?
Gaskiya bana cikin kowacce kungiya ta wasu marubuta.
A rayuwa kuma wanne kalar tufa ka fi so?
Gaskiya na fi sha’awar manyan kaya domin ya fi fito da cikar kamala da kuma haiba ta mutum.
Wanna irin abinci ka fi sha’awa?
Wake da shinkafa.
Wace irin mota ta fi burge ka?
Abin da ba ka da shi bar shi a ba ka so.
To Malam Alkasim mun gode.
Ni ne da godiya.