• English
  • Business News
Saturday, October 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Za A Iya Rasa Adalci Wajen Warware Matsalar Falasdinu Ba

by CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Ba Za A Iya Rasa Adalci Wajen Warware Matsalar Falasdinu Ba
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo

Xi Ya Taya Grand Duke Guillaume Na Luxembourg Murnar Hawa Karagar Mulki

Jiya Alhamis, 30 ga watan Mayu, yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza da ke da nisan dubban kilomita daga birnin Beijing, taron ministoci karo na 10 na dandalin tattauna hadin-kan Sin da kasashen Larabawa, ya fitar da hadaddiyar sanarwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa kan batun Falasdinu, inda suka fitar da wata murya, don sa kaimi ga warware rikicin Gaza cikin gaggawa da kuma warware matsalar Palasdinu cikin adalci, da samar da mafita mai dorewa.

Yayin da yanayin da ake ciki tsakanin Falasdinu da Isra’ila ke kara tabarbarewa, taron ministocin karo na 10 na dandalin tattauna hadin-kan kasar Sin da kasashen Larabawa ya gabatar da kira mafi girma na tsayawa tsayin daka kan mara baya ga al’ummar Palasdinu wajen maido da hakkinsu na kasa baki daya, wadda ta samu kulawa sosai daga wajen kasashen duniya.

  • Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Tunisia Kais Saied
  • Li Qiang Ya Mika Sakon Murna Ga Sabon Firaministan Kasar Chadi

“Yaki ba zai iya ci gaba da wanzuwa har abada ba, ba za a rasa adalci har abada ba, kuma ba za a iya girgiza shirin ‘kasashen biyu’ ba”, shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya bayyana haka a cikin muhimmin jawabin da ya gabatar a bikin bude wannan taro, wanda ya ja hankalin jama’a.

Batun Falasdinawa dai shi ne jigon batun Gabas ta Tsakiya. Ko yaya yanayin kasa da kasa ya canza, kasar Sin tana goyon bayan maido da halaltaccen hakkin al’ummar Palasdinu. Za kuma ta ci gaba da tsayawa tare da kasashen Larabawa, da tabbatar da adalci, da kokarin ganin an tsagaita bude wuta ba tare da wani sharadi ba cikin gaggawa tsakanin Falasdinu da Isra’ila, kana da inganta warware rikicin Palasdinu cikin daidaito da adalci da zai dore, da samar da zaman lafiya na hakika a yankin Gabas ta Tsakiya da ke cikin mawuyacin yanayi sakamakon yaki. (Bilkisu Xin)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: FalasdinuGazaHamasIsra'ila
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ministocin Tsaron Sin Da Amurka Sun Gana A Kasar Singapore

Next Post

Masu Baje Kolin Kaya Kimanin 300 Za Su Halarci Bikin Kasuwancin Yammacin Afirka A Legas

Related

Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo
Daga Birnin Sin

Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo

17 hours ago
Xi Ya Taya Grand Duke Guillaume Na Luxembourg Murnar Hawa Karagar Mulki
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Grand Duke Guillaume Na Luxembourg Murnar Hawa Karagar Mulki

18 hours ago
Sabbin Gonakin Da Za A Magance Zaizayewar Kasa A Sin A Karshen Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Na 14 Sun Kai Muraba’in Kilomita 340,000
Daga Birnin Sin

Sabbin Gonakin Da Za A Magance Zaizayewar Kasa A Sin A Karshen Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Na 14 Sun Kai Muraba’in Kilomita 340,000

19 hours ago
Jami’in MDD: Kayataccen Hutun “Golden Week Plus” Na Kasar Sin Ya Nuna Tasirin Yawon Bude Ido A Duniya 
Daga Birnin Sin

Jami’in MDD: Kayataccen Hutun “Golden Week Plus” Na Kasar Sin Ya Nuna Tasirin Yawon Bude Ido A Duniya 

20 hours ago
Xi Da Takwaransa Na Singapore Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 35 Da Kulla Huldar Diflomasiyya
Daga Birnin Sin

Xi Da Takwaransa Na Singapore Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 35 Da Kulla Huldar Diflomasiyya

22 hours ago
Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin

2 days ago
Next Post
legas

Masu Baje Kolin Kaya Kimanin 300 Za Su Halarci Bikin Kasuwancin Yammacin Afirka A Legas

LABARAI MASU NASABA

Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu

Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu

October 4, 2025
Ƴar Wasan Gaban Nijeriya, Ifeoma Onumonu Ta Yi Ritaya

Ƴar Wasan Gaban Nijeriya, Ifeoma Onumonu Ta Yi Ritaya

October 4, 2025
Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)

Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)

October 4, 2025
Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ

October 4, 2025
Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Gwamnatin Jigawa Ta Bai Wa  Mahaddata Ƙur’ani 200 Tallafin Karatu

Gwamnatin Jigawa Ta Bai Wa  Mahaddata Ƙur’ani 200 Tallafin Karatu

October 4, 2025
Ruwan Sama Ya Lalata Gadoji Da Hanyoyi A Taraba, Kebbi Da Filato

Ruwan Sama Ya Lalata Gadoji Da Hanyoyi A Taraba, Kebbi Da Filato

October 4, 2025
Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet

Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet

October 4, 2025
Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

October 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi

October 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.