Hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin, da hukumar hadin gwiwar neman ci gaban kasa da kasa ta kasar, sun kaddamar da wani sansanin ba da horo a fannin mu’amala, da hadin gwiwa ta fuskar samar da ci gaban harkokin mata na kasa da kasa.
Hausawa kan ce ilmantar da mace guda, tamkar ilmantar da al’umma ne. Kamar yadda takwarorinsu maza suke taka rawa a harkokin da suka shafi shugabanci da tsara manufofi, su ma mata idan suka samu dama, za su iya bayar da kwatankwacin gudunmawar.
- ‘Yan Kasuwar Afrika Sun Gano Zarafi Mai Kyau A Canton Fair
- Shugaban Serbia: Zan Rubuta Wani Littafi Don Tunawa Da Hulda Ta Da Xi Jinping
Baya ga tallafawa a bangarori kamar na bunkasa tattalin arziki da ababen more rayuwa da sauransu, kasar Sin tana kuma mayar da hankali kan kowanne bangare da zai taimaka ga samar da ci gaba na bai daya, shi ya sa a ko da yaushe na kan bayyana ta a matsayin mai hangen nesa da kaifin basira. A zamana a kasar, na ga yadda ake bayar da muhimmanci ga harkokin mata da yadda ake ba su damarmaki daidai da takwarorinsu ba tare da nuna musu wariya ba. Kuma na ga yadda hakan ya ba mata damar taka rawa a fannoni daban-daban kama daga kimiyya da fasaha da tattalin arzikin da harkokin shugabanci da sauransu, har ma da yadda suka bayar da gudunmawa wajen fatattakar talauci, shi ya sa ba za a taba raba ci gaban da kasar Sin ta samu da gudunmawar mata ba.
Ina da yakinin cewa, rawar da mata a kasar Sin ke takawa sakamakon damarmakin da aka ba su ne ya sa kasar ke wa kasashe masu tasowa sha’awar irin hakan. Duk da cewa, an bar mata a baya cikin al’amuran da suka shafi tafiyar da harkokin kasashe da ma duniya, lokaci bai kure ba na damawa da su.
Ba shakka, wannan yunkuri na kungiyar mata ta kasar Sin da hukumar neman ci gaban kasa da kasa ta kasar, ya bullo da kyakkyawar dabarar da za ta ba mata kwarin gwiwa, musamman na kasashenmu masu tasowa, ta yadda za su shiga a dama da su cikin muhimman harkokin kasa tare da bayar da irin nasu gudummawa ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasashensu. (Faeza Mustapha)